Budurwa ‘Yar Najeriya Na Biyan N335k Na Hayar Daki Daya Duk Wata A UK, Ta Yi Bidiyon Cikin Gidan

Budurwa ‘Yar Najeriya Na Biyan N335k Na Hayar Daki Daya Duk Wata A UK, Ta Yi Bidiyon Cikin Gidan

  • Wata matashiya yar Najeriya ta haddasa cece-kuce bayan ta bayyana cewa tana biyan N335k kudin hayar daki daya duk wata a UK
  • A cikin dakin akwai dan karamin gado irin na yan makaranta yayin da mutane ke al’ajabin har nawa take samu da take biyan wannan makudan kudade
  • Da take martani, budurwar ta bayyana cewa koda dai za ta iya biyan kudin, a kullun tana jin takaicin yadda ake cire kudade daga albashinta

Birtaniya - Wata matashiyar budurwa yar Najeriya wacce ke zama a Birtaniya ta bayyana yawan kudin da take biya na hayar gida mai daki daya a kasar wajen.

Da take bidiyon dan karamin gidan, budurwar ta bayyana cewa a duk wata tana biyan hayar £399 (N335,033.118). Gidan na dauke da dan karamin gado a gefe daya.

Kara karanta wannan

Karfin hali: An kama wani sojan bogi da ke yiwa mata fashi da makami

Budurwa da daki
Budurwa ‘Yar Najeriya Na Biyan N335k Na Hayar Daki Daya A UK, Ta Yi Bidiyon Cikin Gidan Hoto: TikTok/@_yinyechiii
Asali: UGC

Rayuwa cikin daki daya a Birtaniya

Wani bangaren na dauke da tebur da dan karamin allo na karatu. Budurwar ta bayyana cewa a nan ne take wasa kwakwalwarta. Ta bayyana cewa bandakinta na da kyau sosai.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewarta, babu bangaren saka kayan sawa don haka ta samawa kayanta inda zai iya daukarsu.

Kalli bidiyon a kasa:

Ga wasu daga cikin martanin jama’a a kasa:

RFF ya ce:

“Baaba, ina dai fatan kina samun abun da ya fi wanda kike kashewa.”

Ta yi martani:

“Eh tabbass ina samu, amma abun na mun ciwo duk wata cewa sai an cire kudin hayar dakin.”

Fashbabz2 ta ce:

“wa ya lura akwai man zafi na aboliki a cikin kwabanta.”

Ta yi martani:

“Aboniki ne fa…Sanyin nan zai saita maka kwakwalwa…Ina ta danasani na dauki da yawa don na dunga siyarwa saboda na lura mutane na bukatar sa.”

Kara karanta wannan

Wata 6: Duk da aikin Hisbah, rahoto ya fadi kudin da 'yan Najeriya suka kashe a shan giya

Raphael Onodu (REON) ya ce:

“Ya yi arha, a kanada, musamman Nova Scotia kudin haya ya kai kimanin $500 zuwa sama duk wata.”

Kudin Haya 2.7m duk shekara, Kudin Diesel N80k: Bidiyon Gidan Mai Dakuna 3 Da Budurwa Ta Gani A Lagas

A wani labarin, wata matashiya yar Najeriya, Anagu Nkemjika, wacce ke neman gidan haya a jihar Lagas ta wallafa bidiyon yawon da ta sha wajen neman gida.

Nkemjika ta bayyana cewa a karshe ta ga irin gidan da take nema kuma kudin hayar gidan duk shekara naira miliyan 2.7 ne kuma yana dauke da dakuna uku.

Ba iya nan abun ya tsaya ba, kudin hayar baya kunshe da kudaden hidindimu N600,000 da kudin man diesel N80,000 duk wata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel