Lokoja: Gwamnatin Kogi ta yi ritaya sakatare na dindindin 8, sa'a nan ta sallami ma'aikata 1,774
- Gwamnatin Kogi ta yi ritaya sakatare na dindindin 8, ta kuma sallami ma'aikata 1,774
- Gwamnati ta shida cewa wadanda lamarin ta shafa an basu wasikarsu a watan Disamba da ta gabata
- Matakin ta shafi sakatare na dindindin da darektoci waɗanda suka yi aiki har shekaru hudu zuwa sama
Gwamnatin Kogi a ranar Lahadi, 7 ga watan Janairu ta tabbatar cewa ta yi ritaya sakatare na dindindin su takwas da wasu darektoci, sa’a nan kuma ta sallami ma’aikata 1, 774 daga ma’aikatar jihar.
Labari ya zo mana daga jaridar NAN cewa ma'aikatan da wannan lamarin ta shafa an basu wasikarsu a watan Disamba da ta gabata.
Shugaban ma’aikata a jihar, Misis Deborah Ogunmola da shugaban hukumar ma’aikata wato ‘Civil Service Commission’ suka sanya hannu a wasikun.
Kwafi na wasiƙar ritaya da aka yi wa ɗaya daga cikin sakataren din din din da lamarin ta shafa ya nuna cewa an yi ritayan ne don amfanin jama'a ne.
KU KARANTA: Akwai bukatar Buhari ya rairaye masu yiwa gwamnatin sa zagon kasa - Chukwuani
Wasu daga cikin sakataren sun shaida wa majiyar Legit.ng cewa suna shawarar zuwa kotu.
Duk da haka, Misis Petra Akinti-Onyegbule, babban sakataren labarai ga gwamna Yahaya Bello, ta kare wannan batun, ta ce matakin na cikin ɓangare na sake fasalin ayyukan ma’aikatar gwamnatin jihar.
A cewar ta, matakin ta shafi sakatare na dindindin waɗanda suka yi aiki har shekaru hudu zuwa sama.
Onyegbule ta kara da cewa, matakin ta kuma shafi darektocin da suka yi aiki har shekaru takwas zuwa sama.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng