Kano: Wata Mota Bas Dauke Da Fasinjoji 15 Ta Kama Da Wuta, An Rasa Rayyuka

Kano: Wata Mota Bas Dauke Da Fasinjoji 15 Ta Kama Da Wuta, An Rasa Rayyuka

  • Hatsarin mota ya yi sanadin rasuwar mutane uku da jikkata wasu da dama a karamar hukumar Takai na Jihar Kano
  • Hatsarin ya faru ne tsakanin wata bus mai dauke da mutum 15 da Toyota Hilux mai dauke da mutum uku
  • Saminu Yusuf, kakakin hukumar kwana-kwana ta Jihar Kano ya tabbatar da afkuwar hatsarin ya kuma bayyana sunayen wadanda suka rasu

Kano - Mutane uku sun rasu, yayin da wasu 15 suka jikkata a wani hatsarin mota da ya faru a karamar hukumar Takai ta Jihar Kano, Daily Trust ta rahoto.

Hukumar kwana-kwana ta Jihar Kano ta tabbatar da afkuwar lamarin ta bakin kakakinta, Mista Saminu Yusuf, a ranar Lahadi.

Taswirar Jihar Kano
Mutane 3 Sun Mutu A Yayin Da Bas Ta Kama Da Wuta A Kano. Hoto: @MobilePunch.
Asali: UGC

Ya ce hatsarin ya ritsa da wata Toyota Hilux ne da ke dauke da mutum 3 daga Jigawa da wata motar bas ta haya mai dauke da mutum 15 daga Kano.

Kara karanta wannan

Daga Karshe: Wata Kabila A Duniya Ta Shafe, Mutum 1 Da Ya Rage Ya Koma Ga Allah

A cewarsa, bayan motoccin sun yi karo, bas din ta kama da wuta kuma aka ceto mutum uku a sume, yayin da sauran suka jikkata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce:

"Bayan samun bayanin, mun tura tawagarmu ta bada dauki cikin gaggawa.
"Da isarsu, sun gano cewa motar bas ta haya (hummer) mara lamba dauke da mutum 15 ce ta yi karo da Toyota Hilux mai dauke da mutum uku daga Jigawa mai lamba JMK 142 XA. Bas din ta kama da wuta.
"Cikin mutum 18 da hatsarin ya ritsa da su, an ceto mutum 15 da ransu yayin da an ceto uku cikin fasinjojin bas din a sume. Nan take muka kai su Babban Asibitin Takai inda likitoci suka tabbatar mutum ukun da aka ceto a sume sun mutu."

Abdullahi ya ce wadanda suka rasun sune Sani Isah, mai shekara 28; Shamawilu Isah, mai shekara 30 da Yusuf Musa, mai shekara 32.

Kara karanta wannan

Karfin hali: An kama wani sojan bogi da ke yiwa mata fashi da makami

Ya shawarci masu motocci su rika taka-tsantsan yayin tuki.

Fitaccen Dan Siyasan Arewa Ya Mutu A Hatsarin Mota

A wani rahoton, kwamishinan Matasa Da Wasanni na Jihar Yobe, Hon. Goni Bukar Lawan, (BUGON) ya mutu a hatsarin mota kan hanyar Damaturu zuwa Kano.

Goni Bukar, tsohon dan majalisar wakilai na tarayya, wanda aka fi sani da BUGOM, ya rasu a daren yau Talata a hanyarsa na zuwa Jihar Kano, Leadership ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel