Daga Shagari Zuwa Buhari: Jerin Shugabannin Najeriya Da Farashin Naira Zuwa Dala A Karkashin Mulkinsu

Daga Shagari Zuwa Buhari: Jerin Shugabannin Najeriya Da Farashin Naira Zuwa Dala A Karkashin Mulkinsu

Tsawon lokaci, ana amfani da darajar kudin kasar wato Naira, a matsayin wani abin dubi yayin da ake nazarin kwazon shugaban kasa.

A yayin da yan Najeriya ke cigaba da nuna damuwarsu kan faduwar darajar Naira idan aka kwatanta da Dala, wani rahoto daga StatiSense, kamfanin tuntuba, ya fitar da jerin shugabannin Najeriya da darajar naira zuwa dala a lokacin mulkinsu.

Shugabannin Najeriya
Daga Shagari Zuwa Buhari: Jerin Shugabannin Najeriya Da Farashin Naira Zuwa Dala A Karkashin Mulkinsu. Hoto: Femi Adesina, Goodluck Jonathan.
Asali: Facebook

StatiSense ta ambaci cewa ta samo alkalluman ne daga babban bankin Najeriya, CBN. Ga jerin darajar naira zuwa dala a kasa:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Shugabannin Najeriya da farashin naira zuwa dala 1 a zamaninsu

  • Shehu Shagari (1 ga watan Oktoban 1979, zuwa 31 ga watan Disamban, 1983): 75kobo
  • Manja Janar Muhammadu (31 ga watan Disamban 1983 zuwa 27 ga watan Agustan 1985) 75kobo - 90kobo
  • Janar Ibrahim Badamasi Babangida, IBB (27 ga watan Agustan 1985 zuwa 27 ga watan Agustan 1993): 90kobo - N21.9kobo
  • Cif Ernest Adekunle Oladeinde Shonekan (26 ga watan Agustan 1993 zuwa 17 ga watan Nuwamban 1993): N21.9kobo
  • Janar Sani Abacha (17 ga watan Nuwamban 1993 zuwa 8 ga watan Yunin 1998): N21.9kobo
  • Janar Abdulsalami Alhaji Abubakar (9 ga watan Yunin 1998 zuwa 29 ga watan Mayun 1999): N21.9kobo - N94.9kobo
  • Cif Olusegun Aremu Okikiola Matthew Obasanjo (mai ritaya) (29 ga watan Mayun 1999 zuwa 29 ga watan Mayun 2007): N94.9kobo - N127.6kobo
  • Umaru Musa Yar'adua (29 ga watan Mayun 2007 zuwa 5 ga watan Mayun 2010): N127.6kobo - N150.3kobo
  • Dakta Goodluck Ebele Jonathan (6 ga watan Mayun 2010 zuwa 29 ga watan Mayun 2015): N150.3kobo - N197.00kobo
  • Muhammadu Buhari (29 ga watan Mayun 2015 zuwa yanzu): N197.00kobo - N422.00kobo

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Daga Karshe, DSS Ta Sako 'Mahaifiyar' Nnamdi Kanu Bayan Tsare Ta Na Wata 3

Abin Lura: Legit.ng ta bada cikakken sunayen shugabannin kasar da lokacin da suka hau mulki da sauka ne daga alkalluman da ta samu daga ofishin sakataren gwamnatin tarayyar Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164