Daga Karshe, DSS Ta Sako 'Mahaifiyar' Nnamdi Kanu Bayan Tsare Ta Na Wata 3

Daga Karshe, DSS Ta Sako 'Mahaifiyar' Nnamdi Kanu Bayan Tsare Ta Na Wata 3

  • Wani labari da zai faranta wa iyalanta rai shine sakin Misis Ukamaka Ejezie, wacce aka fi sani da Mama Biafra
  • Yar gani kashe-nin na kungiyar IPOB ta samu yanci ne bayan tsare ta da aka ce hukumar Yan sandan farin kaya DSS, ta yi
  • Ifeanyi Ejiofor, shugaban lauyoyin kungiyar masu neman kafa Biafra, IPOB, ne ya bayyana hakan cikin sanarwa da ya fitar a safiyar ranar Lahadi, 28 ga watan Agusta

FCT Abuja - Bayan watanni uku a tsare, DSS ta sako fitacciyar mai goyon bayan kungiyar IPOB, Madam Ukamaka Ejezie wacce aka fi sani da Mama Biafra.

Mama Biafra.
DSS Ta Sako 'Mahaifiyar' Nnamdi Kanu Bayan Tsare Ta Na Wata 3. Hoto: @TheNationNews.
Asali: Twitter

Dattujuwan da aka ce shugaban haramtacciyar kungiyar na IPOB, Nnamdi Kanu ya dauke ta matsayin mahaifiyarsa ta shaki iskar yanci ne a ranar Asabar da yamma.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Hukumar DSS Ta Saki Fitacciyar Mai Goyon Bayan Ƙungiyar 'Yan Ta'adda a Najeriya

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

An kama ta ne a ranar 18 ga watan Mayun 2022, ranar da Kanu ya gurfana a kotu na karshe.

Lauyan Kanu, Ifeanyi Ejiofor ya tabbatar da sakinta cikin wani sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, The Nation ta rahoto.

Ya ce:

"An kama ta ne ranar 18 ga watan Mayun 2022 a harabar kotu, bayan an kammala sauraron shari'ar Nnamdi Kanu a ranar a Abuja."

Ya cigaba da cewa:

"Ina farin cikin sanar da ku cewa an saki Misis Ukamaka Ejezie (Mama Biafra). Yanzu ta fito daga hannun DSS.
"Mun gode wa ChukwuOkike Abiama bisa wannan babban nasarar. Ba za mu gaza ba, duk wani wanda aka tsare har da wanda muke kare wa, Onyendu Mazi Nnamdi Kanu, za su samu yanci nan bada dadewa ba.
"Mu lauyoyi, muna duk abin da za mu iya bisa doka don ganin hakan ya faru, ina tabbatar muku hakan."

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Allah Ya Yiwa Sarkin Funukaye, Alhaji Muhammad Muazu Kwaranga, rasuwa

Azaba Na Ke Sha a Hannun DSS: Nnamdi Kanu Ya Roƙi a Tura Shi Gidan Yari

A wani labarin, shugaban na haramtaciyyar kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, ya roki babban kotun tarayya da ke Abuja ta tura shi gidan gyaran tarbiyya da ke Kuje a Abuja, Daily Trust ta ruwaito.

Kanu, wanda aka sake kamowa sannan aka dawo da shi Nigeria a watan da ta gabata, a halin yanzu yana hannun hukumar yan sandan farin kaya, DSS.

Bayan an dawo da shi kasar Mai Shari'a Binta Nyako, wacce ta bashi beli tunda farko kan dalilin rashin lafiya kafin ya gudu a 2017, ta bada umurnin a tsare shi hannun DSS har ranar 27 ga watan Yuli.

Asali: Legit.ng

Online view pixel