Tsawa Ta Halaka Ango A Yayin Daukar Hotunan Kafin Aure Tare Da Amaryarsa

Tsawa Ta Halaka Ango A Yayin Daukar Hotunan Kafin Aure Tare Da Amaryarsa

  • Wani mai shirin zama ango ta hadu da ajalinsa a wajen daukar hotunan kafin aure tare da amaryarsa
  • Marigayin da budurwarsa sun je shahararren wajen yawon bude ido na kasar China don daukar hotuna ana tsaka da ruwan sama, sai tsawa ta sauka a kansa
  • Hukumomi a kasar sun yi gargadi tun farko game da hatsarin yanayin wanda shine na uku mafi girma a tsarin yanayin kasar

China - Wani mai shirin zama ango ya mutu bayan tsawa ta fada masa a yayin daukar hotunan kafin aure tare da amaryarsa a wani shahararren wajen shakatawa a kasar China.

Mummunan al’amarin ya afku ne a tsaunin Jade na kasar China da ke lardin Yunnan a makon jiya.

Ruwan sama
Tsawa Ta Halaka Ango A Yayin Daukar Hotunan Kafin Aure Tare Da Amaryarsa Hoto: LIB
Asali: UGC

An yi gaggawan kwasar mutumin mai suna Ruan zuwa asibiti inda aka tabbatar da ya rasu, jaridar South China Morning Post ta rahoto.

Kafin tsawar ta saukar masa, hukumomin kasar China sun yi gargadi game da yanayi mai launin dorawa, wanda shine na uku wajen girma a tsarin yanayin kasar, shafin LIB ya rahoto.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Duk da tsawar da aka ta yi, masu shirin zama ma’auratan sun ci gaba da shirinsu na zuwa daukar hotunan.

An gano yadda tawagar ceto dauke da gawar mutumin kan gadon daukar marasa lafiya a cikin ruwan sama tsamo-tsamo.

Kyawawan Hotunan Daurin Auren Wasu Yan Najeriya A Dubai Ya Yadu, Sun Yi Shaglin Bikinsu A Saukake

A wani labari na daban, wani dan Najeriya mai suna Duru C.E. ya angwance da kyakkyawar budurwarsa a Hadaddiyar Daular Larabawa.

Sai dai wasu mutane sun lura cewa babu wasu baki da suka halarci daurin auren yayin da aka gano mutumin tare da matarsa kadai a wajen karbar takardar shaidar zama ma’aurata.

Sai dai kuma, Duru ya ce akwai gagarumin shagalin bikin da zai zo a nan gaba bayan masu amfani da Twitter sun fara sharhi game da yadda ya yi bikinsa cikin sauki baki a lekun daga shi dai amaryarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel