Sunayen Jihohi 7 da Kananan Hukumominsu da 'Yan Ta'adda ke Barazanar Hana Zaben 2023

Sunayen Jihohi 7 da Kananan Hukumominsu da 'Yan Ta'adda ke Barazanar Hana Zaben 2023

  • Rashin tsaro a kowacce rana kara kamari yake a wasu jihohin kasar nan yayin da hakan ke zama barazana ga zaben 2023
  • Kamar yadda aka gano, akwai jerin jihohin Kaduna, Zamfara, Katsina, Imo, Abia, Niger da Sokoto da 'yan ta'adda ba dole su bari a yi zabe ba a wasu sassan
  • Akwai sama da kananan hukumomin jihohin bakwai har 40 da 'yan ta'addan suka kwace suke cin karensu babu babbaka

Al'amarin rashin tsaro a Najeriya ya dauka fuskar ban tsoro ta yadda sama da kananan hukumomi 40 a sassa daban-daban na kasar nan ke karkasin ikon 'yan bindiga, 'yan ta'adda da 'yan bindigan da ba a sani ba.

Wuraren dake karkashin ikon 'yan ta'addan suna cikin jihohin Kaduna, Zamfara, Niger, Katsina, Sokoto, Abia da Imo.

Kara karanta wannan

'Yan Sanda Sun Magantu Kan Batun Kama Bakin Haure Suna Dillancin Makamai da Helikwafta

Wannan lamari babu shakka babbar barazana ce ga zaben 2023 ballantana tsaron ma'aikatan zabe da masu kada kuri'u a inda 'yan ta'adda ke mulka ba abu bane mai tabbas.

'Yan bindiga sun kwace wasu kananan hukumomi a jihar Kaduna

A jihar Kaduna, wasu kauyukan jihar duk jama'a sun bar su sakamakon lamurran ta'addanci a jihar, Punch ta rahoto hakan.

Kananan hukumomi kamar Chikun, Kajuru, Kachia, Zangon Kataf, Kauru, Lere, Birnin Gwari da Giwa duk suna fuskantar farmakin 'yan ta'adda.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kananan hukumomin Zamfara

Zamfara tana daga cikin jihohin da ta'addancin 'yan bindiga da 'yan ta'adda yayi kamari kuma za a iya cewa suna cin karensu babu babbaka a dukkan kananan hukumomin jihar.

Daga cikin kananan hukumomin da lamarin yafi kamari akwai: Maru, Tsafe, Bakura, Anka, Maradun, Gusau, Bukkuyum, Shinkafi da Bungudu.

A yayin zantawa da jaridar Punch, wani mazaunin kauyen Babbar Doka dake karamar hukumar Maru, Malam Ibrahim Abubakar, yace zai yi wuya su iya fita zaben 2023.

Kara karanta wannan

Ana Zargin Matar Aure Da Kashe Mijinta A Jihar Kebbi, Yan Sanda Sun Damketa

Kananan hukumomi 7 daga jihar Niger

A jihar Niger, kananan hukumomi bakwai ne ke fama da hare-haren 'yan ta'addan. Sun hada da Rafi, Munyan, Shiroro, Magama, Mashegu, Mariaga da Wushishi yayin da 'yan Boko Haram suka kafa tuta a Shiroro.

Wasu daga cikin jama'ar yankunan sun ce sun gigice sakamakon rashin tsaro wanda yasa suka tsere tare da barin gidajensu.

Kananan hukumomin Katsina

Bincike ya nuna cewa, 'yan ta'adda sun kara yawan wuraren suke kai hari bayan kananan hukumomi takwas da suke cin karensu babu babbaka a Katsina.

Kananan hukumomin sune: Batsari, Jibia, Danmusa, Safana, Kankara, Dandume da Faskari inda suka zarta har Dutsinma, Kurfi, Batagarawa, Rimi, Danja, Kafur, Matazu, Kaita, Malumfashi da Katsina.

Sokoto

A kalla kananan hukumomi 11 daga cikin 23 na jihar Sokoto suna fama da rashin tsaro. Kananan hukumomin da lamarin ya shafa sun hada da Illela, Rabah, Sabon-birni, Isa, Wurno, Gada da Goronyo.

Sauran sun hada da Tangaza, Gudu, Denge-shuni da Kebbe yayin da Shagari da Yabo farmakin bai tsananta ba.

Kara karanta wannan

Manyan 'Yan Ta'adda 8 Sun Shiga Hannun Dogaran Fadar Shugaban Kasa a Abuja

Wasu mazauna yankin sun bayyana tsoronsu kan yadda rashin tsaron ke cigaba da kamari wanda babu shakka barazana ne ga zaben 2023.

Rashin tsaron jihar Abia

Rashin tsaron da ya fara addabar kananan hukumomin Isuikwuato da Umunneochi ba zai hana zaben 2023 idan gwamnatoci a kowanne mataki suka samar da tsaron da ya dace kamar yadda wani shugaban yankin Isuochi, karamar hukumar Umunneochi, Cif Nnokwam Ogbonna ya tabbatar.

'Yan ta'addan Imo

Lamurran 'yan ta'adda a kananan hukumomin Orsu, Orlu, Oru East, Oru ta yamma da wasu sassan karamar hukumar Njaba a jihar Imo sun zamo abun damuwa ga mazauna yankin dake shirin zaben 2023.

Yayin da wasu suka arce suka bar yankunan saboda kashe-kashe da kone-konen hukumomin tsaro da kayan gwamnati, akwai tantama idan za a yi zabukan 2023 a wuraren.

Asali: Legit.ng

Online view pixel