Manyan 'Yan Ta'adda 8 Sun Shiga Hannun Dogaran Fadar Shugaban Kasa a Abuja
- Hedkwatar Tsaro ta Najeriya tace dakarun sojoji sun damke manyan 'yan ta'adda 8 a babban birnin tarayya na Abuja
- Gagarumin aikin kamar yadda shugaban rundunar ya bayyana, dogaran fadar shugaban kasa ne suka yi shi a Deidei Abbatoir da kauyen Dukpa daka Gwagwalada
- An yi wannan aiiki ne kasa da watanni biyu bayan sojojin fadar shugaban kasa 8 sun halaka a wani farmaki da 'yan ta'adda suka kai musu
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
FCT, Abuja - Rundunar sojin Najeriya ta kai samame maboyar 'yan ta'adda inda suka cafke manyan 'yan ta'adda takwas a yankin.
Hedkwatar tsaro ta bayyana hakan ne a ranar Alhamis, 25 ga watan Augustan 2022 inda ta kara da cewa an kama 'yan ta'addan ne a maboyarsu dake Deidei Abbatoir da kauyen Dukpa a karamar hukumar Gwagwalada, The Nation ta rahoto.
Dakarun fadar shugaban kasan ne suka aiwatar da aikin.
Idan za a tuna, hafsoshin soji biyu da sojoji shida daga cikin dogaran fadar shugaban kasan sun rasa rayukansu sakamakon harin kwanton bauna da 'yan ta'adda suka kai yankin Bwari.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
An gano cewa a sansanin ne 'yan Boko Haram da mambobin ISWAP ke kafa dandalinsu.
Kamar yadda daraktan yada labarai na rundunar, Manjo Janar Musa Danmadami ya bayyana, an kai samamen a ranar 13 ga watan Augusta.
“A samamen, mutum takwas aka kama da zargin ta'addanci, bindigu kirar AK47 guda biyar da wasu guda uku aka samu."
Yadda Shehin Malami ya Taimaki Wanda Bai Sani ba, Ya Kare da Halaka shi
A wani labari na daban, an kara samun bayanai kan mutuwar Sheikh Goni Aisami, fitaccen malamin addinin Islama na Yobe jihar Yobe wanda aka bindige a ranar Juma'a.
Kamar yadda DSP Dungus Abdulkarim, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Yobe ya bayyana, mutum biyun da ake zargi sojoji ne daga bataliya ta 241 sake Recce a Nguru sun shiga hannu.
Daily Trust ta rahoto cewa, yace lamarin ya faru wurin karfe 10 na daren Juma'a bayan Aisami ya ragewa daya daga cikin wadanda ake zargin hanya.
Kakakin rundunar 'yan sandan yace Aisami na tuka motar daga Gashua zuwa Nguru, lokacin da wanda aka zargin ya tsayar da shi da kayan gida dauke da gado kuma ya roki malamin da ya rage masa hanya zuwa Jaji-Maji.
Asali: Legit.ng