Cike da Kwarin Guiwa, Dalibi Ya Nemi Malamarsa Da Ta Aureshi, Bidiyon Ya Bada Mamaki
- Bidiyon neman aure na wani dalibin makaranta da malamarsa ya bayyana a shafukan soshiyal midiya
- A cikin bidiyon, an gano yaron wanda ya kasance bakin fata tsugune a gaban malamar tasa cike da kwarin guiwa a gaban sauran dalibai
- Wannan bukata tasa ya jefa dalibai cikin murna, yayin da malamar ta jefa hannu a sama cike da farin ciki
Wani dalibin makaranta ya nemi malamarsa ta aure shi a cikin wani bidiyo da ya sanya mutane da dama tofa albarkacin bakunansu.
Dan gajeren bidiyon da shafin @stjrbu ya wallafa a TikTok ya nuno yaron sanye da kayan makaranta fari da baki tsugune a kan guiwarsa sannan ya gabatarwa malamarsa da zobe na neman aurenta.
Wannan karfin guiwa na yaron ya burge daliban da ke wajen sannan ya jefa su cikin yanayi na farin ciki.
Ya baiwa malamar mamaki
Yayin da malamar wacce ta cika da mamaki ta juya baya, sai matashin wanda ya kasance bakar fata ya tashi sannan ya sake fuskantarta da zoben yayin da ya sake tsugunawa a kan guwiwarsa.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
An jiyo muryar wata budurwa a kasa tana umurtan malamar da ta ce eh.
Yayin da daliban ke ci gaba da murna, cike da mamaki sai malamar ta jefa hannunta a sama ba tare da ta karbi zoben ba.
A lokacin da ta aikata haka, sai yaron ya tashi tsaye sannan dalibai maza suka rungume shi cike da murna. Ba a nuna a wani makaranta ne abun ya faru ba ko kuma lamarin wasa ne.
Kalli bidiyon a kasa:
Jama’a sun yi martani
MoJo007 ya ce:
“Malama mai tsananin saukin kai, tana da kyau da ban dariya.”
sophiefarrell37 ta ce:
“Wayyo Allah na kasa yarda da gaske auren malama za ka nema.”
{Queenbeelizzy} ta ce:
“Dan uwa ya kai Kaman 16 sannan malamarsa kamar 47 banbancin shekaru bai da wani yawa kawai kamar shekaru 31 ne ina gani.”
dux • Follows You ya ce:
"Emmanuel Macron ya auri malamarsa sannan daga baya ya zama shugaban kasarsa. Komai mai yiwuwa ne idan ka je masa.”
Haduwar TikTok: Bidiyon Baturiya Da Ta Baro Kasarta Don Kasancewa Da Wani Kyakkyawan Saurayi, Ta Haifa Masa Da
A wani labarin, wani soyayya da aka fara kamar wasa a dandalin TikTok ya yi karfi har ya kai ga aure.
Dammy, wani matashi daga Ivory Coast ya ce ya fada soyayyar matarsa Baturiya mai suna Laura bayan ta wallafa wani bidiyo game da cin zarafin gidan aure sai ya yi martani a kai.
Daga bisani sai masoyan biyu suka fara bin junansu a dandalin kuma sai alaka mai karfi ta shiga tsakaninsu.
Asali: Legit.ng