Kisan Malami: Da Musulmai Suka Kashe Fasto, da Batun Ya Canza - Bala Lau Ya Dauki Zafi
- Sheikh Abdullahi Bala Lau ya tabbatar da cewa Musulmai ba za su yarda da kisan da aka yi wa Sheikh Goni Aisami a jihar Yobe ba
- Kungiyar Jama’atul Izalatul Bidi’a Wa Iqamatus Sunnah tana zargin ana yi wa Musulmai ta’addanci, tace sam ba za a hakura ba
- Shi ma Dr. Khalid Abubakar Aliyu na kungiyar Jama’atu Nasirl Islam yace idan da Fasto aka kashe, da CAN tayi ta yin maganganu
Abuja - Shugaban kungiyar Izala, Sheikh Abdullahi Bala Lau ya yi karin bayani game da kisan shehin malami, Sheikh Goni Aisami da aka yi a jihar Yobe.
Sheikh Abdullahi Bala Lau ya yi magana da BBC Hausa a ranar Laraba, 24 ga watan Agustan 2022, yace kisan malamin rashi ne ga Duniyar Musulmai.
A tattaunawar da aka yi da shi, Bala Lau ya sha alwashin cewa ba za su yi yarda da wannan ta’addanci ba, yace ba za su yi shiru maganar ta mutu ba.
Daily Trust ta bi hirar da aka yi, tace shugaban kungiyar ta JIBWIS ya bukaci a bi diddikin abin da ya jawo aka hallaka wannan mutumi kan hanya.
Shugaban kungiyar ta Izala ya zargi wadanda suka yi wannan da ta’addanci a kan Musulmai.
An yi babban rashi - Bala Lau
“Wannan babban rashi ne ga duka Musulmai, yadda aka kashe shi ya nuna ta’addanci ake nufi a kan al’ummar Musulmai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Muna Allah-wadai da kisan na shi, kuma muna nuna matsayinmu cewa dole gwamnatin tarayya ta dage wajen ganowa da daukar mataki.
A binciki abin da ya sa suka hallaka shi. Yau da wadanda suka yi wannan kisan Musulmai ne, da sai a dauke shi da wani abin dabam.
Yau da wani Musulmi suka kashe malamin kirista, da ka ji abubuwa sun canza a cikin kasa. Ba za mu bari ba, ba za mu yi shiru ba.
Za mu cigaba da neman hakkin wannnan malami. - Bala Lau.
Bala Lau yace tun da an cafke wadanda ake zargi, ya kamata a hukunta su, akasin abin da ya faru wajen kisan su Jafar Adam da Auwal Albani.
Martanin Jama’atu Nasirl Islam (JNI)
A daidai wannan lokaci aka samu rahoto an kama sojoji biyu da laifi, har Jama’atu Nasirl Islam (JNI) ta yi kira ga hukumta ta hukunta masu laifin.
Sakataren JNI na kasa, Dr. Khalid Abubakar Aliyu ya fitar da jawabi yana alhinin irin kisan gillar, yace da wani Fasto aka kashe, da CAN tayi ta surutu.
Asali: Legit.ng