Gwamnatin Najeriya Za Ta Dauki Malamai da Masu Sana’ar Hannu Tura Su Aiki a Kasashen Waje
- Gwamnatin Buhari na neman ’yan Najeriyan da suka cancanta da su cike a takardun neman aiki a fannin koyarwa da likitanci da dai sauransu
- Gwamnati za ta dauki ma'aikata ne ta tura su zuwa bangarori daban-daban a jamhuriyar Benin, Nijar, Uganda, Seychelles, Zanzibar da Jamaica
- Wannan dai wani shiri ne muhimmi a manufar Najeriya na hulda da kasashen ketare, wanda aka shirya don karfafa alaka da sauran kasashen duniya
FCT, Abuja - Hukumar agajin fasaha ta DTAC, ma’aikatar harkokin waje ta nemi hazikan ’yan Najeriya da su cike foma-foman neman aiki a fannonin koyarwa da likitanci.
Hukumar ta ce, wadanda aka dauka aiki za su tafi cibiyoyi daban-daban a jamhuriyar Benin, Nijar, Uganda, Seychelles, Zanzibar da Jamaica domin aiki a can, kamar yadda Legit.ng ta samo.
Ana bukatar kwararru ne a fannoni daban-daban kimiyyar lafiya a fannoni, injiniyanci da fasaha, makarantun harkar ruwa, kimiyya da ilimi, kimiyyar dudanarwa, albarkatun kasa da kimiyyar muhalli har ma da masu sana'ar hannu.
Yadda za a cike aikin
Za a rufe cike wannan aiki ne a ranar Juma'a, 16 ga watan Satumba, kuma za a cike aikin ne ta kafar yanar gizo, sannan a tura takardu ga hukumar.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Mai sha'awar cika aiki zai iya kai takardunsa hukumar da ke Abuja ko kuma ya tura ta imel din nan info@dtac.gov.ng. Kuma cika wannan aiki kyauta ne.
A bara, DTAC ta tura 'yan Najeriya 33 zuwa Uganda, an kuma tura wasu zuwa wasu sassa daban-daban na nahiyar Afrika.
Kamfanin Mai Na NNPC Ya Lissafa Ayyuka 10 da Ya Yi da N2.3trn Na Mai a 2022
A wani labarin, Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPC) ya ba da bahasin dalilin da ya sa har yanzu bai tura ko kobo daga kudaden cinikin mai tun farkon 2022 zuwa yanzu ba.
A jadawalin da ya fitar, NNPC ya bayyana dalla-dalla inda kukaden suka yi a cikin wani daftarin FAAC na watan Yuli a kafar yanar gizo.
Daftarin ya nuna cewa, tsakanin man dan mai da gas, NNPC ya tara kudaden da suka kai akalla Naira tiriliyan 2.38 daga watan Janairu zuwa Yunin 2022.
Asali: Legit.ng