Fatun Layya: Kungiyar Izala Ta Tara Naira Miliyan 107 Bana

Fatun Layya: Kungiyar Izala Ta Tara Naira Miliyan 107 Bana

  • Sakamakon tara fatun Layyan babbar Sallar da ta gabata, kungiyar Izalah ta tara sama da milyan dari
  • Sheikh Abdullahi Bala Lau ya yabawa al'ummar kasar matuka wajen bada hadin kai a wannan aikin tare da tabbatar da gudanar da kudaden kamar yadda yakamata
  • Kungiyar ta gudanar da ayyuka da dama da wadannan kudaden layya a shekarun baya

Kungiyar yada da'awar addinin Musulunci, Jama'atu Izalatul Bid'a wa iqaamatus Sunnah watau JIBWIS ta bayyana cewa ta samu naira miliyan dari da bakwai (₦107,704,484.25) na tattara fatun layyan shekarar 1443AH..

Shugaban kungiyar Izala Ash-Sheikh Dr. Imam Abdullahi Bala Lau ya karbi rahoton kwamitin karban sadakar fatun layya. Kwamitin ya karbi fatun dabbobi a sallar layya da ya gabata a duk fadin jihohin Nijeriya, kungiyar ta bayyana.

Kara karanta wannan

Masoyin Inyamurai ne: Jigon NNPP ya fadi abin da Kwankwaso ya shirya yiwa Inyamurai

Kungiyar ta bayyana hakan ne a jawabin da ta saki a shafin ra'ayi da sada zumuntarta a ranar Laraba, 24 Agusta, 2022.

BAla Lau
Fatun Layya: Kungiyar Izala Ta Tara Naira Miliyan 107 Bana Hoto: NTA
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar jawabin:

"A bana Jihar da tafi ko wace jiha kawo kudi itace jihar Sokoto inda ta tara Naira miliyan goma sha uku da dubu dari takwas da tamanin da shida da naira hamsin kacal (13,886,050,00)
Jihar kaduna ita tayi na biyu inda ta tara fatun Naira miliyan goma sha uku da dubu dari uku da talatin da tara da naira dari shida kacal. (₦13,339,600.00).
Jihar Kebbi ita tayi na uku inda ta tara fatun Naira miliyan goma da dubu dari da sha biyar da naira dari biyu da tamanin kacal. (₦10,115,280,00)
Haka lamarin ya gudana a dukkan jihohin Naijeria talatin da shida harda Abuja."

Kungiyar ta kara da cewa a baya angina katafaren masallaci da gidan shan magani gami da katafaren masaukin baki a cikin birnin Abuja duka da kudaden fatun layyan da jama'a ke badawa.

Kara karanta wannan

Yar-Shekara-12 Kuma 'Yar JSS1 Ta Samu Admishon Shiga Jami'a Saboda Kwakwalwarta

An bude katafaren Masallacin da hedkwatar Izalah ta gina da fatun Layya a Abuja

Shugaba Muhammadu Buhari ya halarci taron bude sabon Masallacin da kungiyar Izalatul ta gina a birnin tarayya Abuja.

An bude Masallacin ne ranar Juma'a, 25 ga Maris, 2022.

Shugaba Muhammadu Buhari ne babban bako na musamman a taron bude Masallacin.

Daga cikin wadanda suka halarci taron bude Masallacin akwai shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmed Lawan; Ministan birnn tarayya Abuja, Muhammad Bello; Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Sultan Sa'ad Abubakar; da Kwamishanan ilimi na biyu na jihar Kano, Alaramma Ahmed Sulaiman, dss.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida

Online view pixel