Ana yi wa Hadimin Buhari Barazana da ICPC Saboda 'Cin' Albashi Bayan Ajiye Aiki
- Human & Environmental Development Agenda (HEDA) ta kai korafi wajen Hukumar ICPC a game da Bashir Ahmaad
- Kungiyar HEDA tana so ayi bincike a kan zargin da ake yi wa Hadimin shugaban kasar na lakume albashi bayan ya bar aiki
- Olanrenwaju Suraju yana so jami’an ICPC su maka Ahmad a gaban kotu idan ta tabbata ya aika laifin da ake zarginsa da shi
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Abuja - Rahotanni sun nuna kungiyar nan ta HEDA mai rajin kare hakkin al’umma ta gabatar da wani korafi gaban hukumar ICPC a kan Bashir Ahmaad.
Vanguard tace kungiyar HEDA ta bukaci a binciki Mai ba shugaban Najeriyan shawara saboda zargin ya karbi albashi a lokacin ya ajiye aikinsa.
Malam Bashir Ahmaad yana cikin wadanda suka yi murabus daga mukamansu domin shiga takara, a karshe ya koma aikinsa bayan ya rasa tikiti.
Ana zargin cewa a sa’ilin da Ahmaad ya yi murabus daga matsayin mai taimakawa Muhammadu Buhari, duk da haka gwamnati ta rika biyansa albashi.
A dalilin wannan ne jaridar The Cable tace an kai karar wannan Bawan Allah ga hukumar ICPC mai yaki da rashin gaskiya, domin ta binciki lamarin.
Jawabin shugaban HEDA, Olanrenwaju Suraju
Shugaban HEDA, Olanrenwaju Suraju ya fitar da jawabi a karshen makon da ya gabata, ya shaida cewa sun roki ICPC suyi bincike na musamman.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Idan har an samu Bashir Ahmaad da laifi, Mista Suraju yana so hukumar ta gurfanar da shi a gaban kotu domin Alkali ya yanke masa hukuncin da ya dace.
"Mun yi rubutu a matsayin jagororin yaki da rashin gaskiya kuma kungiya mai rajin kare hakkin al’umma da tabbatar da gaskiya da adalci a Najeriya da Afrika kamar yadda ka’idojin kasashen Duniya suka tanada, mu na so ayi binciken kwa-kwaf kuma a hukunta Bashir Ahmaad, idan sae shi da laifi."
- Olanrenwaju Suraju
Ba mu saki layi ba inji HEDA
Jaridar ta The Cable ta kara da cewa Suraju ya sha alwashi HEDA ba za tayi kasa a gwiwa ba wajen yakar rashin gaskiya da kare hakkin al’umma.
Bugu da kari, kungiyar tana nan a kan bakarta na ganin ayi gaskiya da wanzar da al’adaci wajen gudanar da gwamnati ba tare da nuna ra’ayin siyasa ba.
Martanin Bashir Ahmaad
Mun tuntubi Ahmaad domin jin gaskiyar zargin da ake yi masa na karbar albashi a watannin Mayu, Yuni da Yuli duk da ya sauka daga kan mukaminsa.
Kamar yadda ya shaidawa Legit.ng Hausa a yammacin Talata, wasu ne suka taso shi a gaba, suna yada munanan labarai a kansa domin su bata masa suna.
Asali: Legit.ng