Rarara Ya Rabu Da Tsohon Mai Gidansa, Ya Koma Bangaren Sharada

Rarara Ya Rabu Da Tsohon Mai Gidansa, Ya Koma Bangaren Sharada

  • Dauda Kahutu Rarara, Shahararren mawakin siyasa ya rabu da tsohon mai gidansa na siyasa ya koma bangaren Sha'aban Sharada
  • Mawakin ya rubuta a shafinsa na soshiyal midiya cewa yana tare da tafiyar Sharada a babban zaben shekarar 2023 da ke tafe
  • A baya-bayan nan, Sha'aban sharada ya fice daga jam'iiyar APC ya koma ADP bayan rasa samun tikitin takarar gwamna

Kano - Fitaccen mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara, wai ya yi watsi da tsohon mai gidansa - Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje, kuma yanzu yana kusantar Sha'aban Sharada, tsohon hadimin Shugaba Muhammadu Buhari, Daily Trust ta rahoto.

Sharada kuma shine ke wakiltar Kano Municipal a Majalisar Tarayya, a baya-bayan nan ya fice daga APC don samun tikitin takarar gwamna a karkashin jam'iyyar ADP.

Kara karanta wannan

Salon Shigar Kashim Shettima Zuwa Taron NBA Ya Dauka Hankulan Jama'a

Rarara. Hoto: @daily_trust.
Rarara Ya Rabu Rabu Da Tsohon Mai Gidansa, Ya Koma Bangaren Sharada. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Instagram, mawakin ya bayyana cewa yana tare da tafiyar Sharada a zaben 2023. A wallafar, mawakin ya yi karin haske kan alakarsa da tsohon mai gidansa, Gwamna Ganduje, rahoton Daily Trust.

"Malam Sha'aban ya zo don ceto Kano ne, idan Kano zai ceto, hakan na nufin kai zai ceto," ya rubuta.

Kazalika, an hangi mawakin yana sauka daga jirgin saman rundunar yan sandan saman Najeriya a cikin wannon makon.

Idan za a iya tunawa, Sha'aban Sharada ya kallubalanci zaben fidda gwani na gwamna na jam'iyyar APC inda mataimakin Ganduje, Nasiru Yusif Gawuna ya yi nasarar zama dan takarar jam'iyyar.

Rarara Ya Shirya Taron Saukar Al-qurani Don Samun Zaman Lafiya A Kasar, Jarumai Maza Da Mata Sun Hallara

A wani rahoton kun ji cewa Shahararren mawakin nan na siyasa kuma shugaban mawakan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Dauda Kahutu Rarara ya gudanar da wani taron addu’a na musamman.

Kara karanta wannan

Rikicin Atiku Da Wike: PDP Za Ta Rasa Mambobi Da Dama A Yayin Da Jerry Gana Yayi Barazanar Fita Daga Jam'iyyar

Rarara wanda ya kuma kasance jagoran tafiyar 13X13 na masana’antar shirya fina-finan Hausa na Kannywood, ya tara malamai inda aka yi saukar Al-Kur’ani mai girma don ci gaban kasar da zaman lafiya.

Kamar yadda jarumi kuma MC Mallam Ibrahim Sharukan ya wallafa a shafinsa na Instagram, ya ce an yanka rakuma biyu bayan addu’an domin tabbatar da zaman lafiyan kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel