Ma’aikata Sun Yi Zanga-Zangar Rashin Biyansu Albashin Shekaru 5 a Kuros Riba

Ma’aikata Sun Yi Zanga-Zangar Rashin Biyansu Albashin Shekaru 5 a Kuros Riba

  • Ma'aikatan gwamnatin jiha a Kuros Riba sun fito domin nuna fushinsu ga rashin samun albashi
  • Ma'aikatan da suka kai 1,700 suk nuna damuwa game da rashin karbar albashi na shekaru biyar jihar
  • Gwamnati ta yi martani, ta ce sam babu ma'aikacin da ke bin gwamantin jiha ko anini, kuma ba a wasa da albashi a jihar

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Kuros Riba - Jaridar PM News ta ruwaito cewa, ma’aikatan gwamnati akalla 1,700 ana jihar Kuros Riba suka fito zanga-zanga a yau Talata 23 ga watan Agusta don nuna damuwa da rashin samun albashi na tsawon shekaru biyar.

An ce 'yan zanga-zangar sun taru ne a sakateriyar jihar tun da karfe 7:30 na safe kuma sun mashigarta ga ma'aikata.

An ga rubuce-rubuce a jikin kwalaye da alluna, inda suke bayyana irin kin amincewarsu da ta hanyar rera wakoki cikin fushi.

Kara karanta wannan

Hotuna: Yadda masoya Peter Obi suka karade titunan garinsu Buhari, suka tsaftace kasuwa

Ma'aikata sun fito zanga-zanga saboda rashin albashi
Ma’aikata Sun Yi Zanga-Zangar Rashin Biyansu Albashin Shekaru 5 a Kuros Riba | Hoto: dailypost.com
Asali: UGC

Wasu daga cikinsu na dauke da allunan da ke tunawa gwamnan jihar irin alkawuran da ya dauka musu, tare da tsokaci ga irin halin kunci da a halin yanzu suke ciki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Na gaba-gaba a zanga-zangar kuma mai magana da yawun tawagar, Mista Raphael Antigha, ya ce tun da ma'aikatan suka kama aiki a tsakanin 2017 zuwa 2018, ba su karbi wani abu da sunan albashi ba.

Dalilin yin zanga-zanga

A cewarsa:

“Mun aikawa gwamnati 'yan aike sau da yawa domin su biya mu hakkinmu amma a kowane lokaci alkawurra kawai ake mana iri daya.
“Gwamnati ta sa an tantance da bincike a kanmu har sau biyu don magance matsalar amma duk da haka, babu abin da za ya sauya.
“An dauke mu aiki a hukumance, kuma an ba mu lambobin aiki har ma da wasikun daukar aiki, kai an ma dauki bayananmu yadda ya kamata.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da 'yan bindiga suka kashe fitaccen lauya a Zamfara

“Mu kusan 1,700 ne kacal kuma mafi yawan albashi a cikinmu shine N47,000.
"Kullum gwamnati na ba da uzurin babu kudi amma duk da haka, yakan ba da daruruwan mukaman siyasa a kowane mako, to a ina yake samo kudin yake biyansu?"

Martanin gwamnati

Sai dai, da yake martani a madadin gwamnatin jihar, shugaban ma’aikata a Kuros Riba, Mista Ogbang Akwaji, ya ce babu ma'aikacin da gwamnati ke bi wani bashin albashi, DailyPost ta ruwaito.

A cewar Ogbang:

“Gwamnatin Kuros Riba jiha daya ce da ta dauki jin dadin ma’aikatanta da daraja sosai, duk kuwa da kalubalen kudaden shiga da ake dashi.
“A yanzu haka, ma'aikatan gwamnatin sun karbi albashinsu na watan Yuli. Babu wasu ma’aikata da ke bin jihar bashin albashi har na shekara biyar.”

Gwamnan El-Rufa'i ya haramta zanga-zanga da sunan addini a jihar Kaduna

A wani labarin, gwamnatin jihar Kaduna a ranar Asabar ta sanar da haramta duk wani zanga-zanga da sunan addini a fadin jihar.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Ma'aikatan muhalli za su rufe dukkan makabartu a Abuja saboda wasu dalilai

Kwamishanan tsaro da harkokin cikin gida na jihar, Samuel Aruwan, a jawabin da ya saki ya bayyana cewa an yanke hakan ne bayan zaman shawara da hukumomin tsaro. Ya bayyana cewa duk wanda ya saba wannan doka zai fuskanci fushin hukuma.

Ya kara da cewa haramta zanga-zangan ya zamto dole bisa abinda ke faru a wasu jihohin Arewacin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.