Matar Aure Ta Gudu Daga Gidan Mijinta, Ta Ce Ba Zata Iya Zama da Yunwa Ba

Matar Aure Ta Gudu Daga Gidan Mijinta, Ta Ce Ba Zata Iya Zama da Yunwa Ba

  • Wani matashi ɗan shekara 30 a duniya ya maka matarsa a Kotun Shari'ar Musulunci ta Kaduna saboda ta gudu daga gidansa
  • Matar ta faɗa wa mai Shari'a cewa tana ƙaunar mijinta kamar yadda yake ƙaunarta amma shi ya ce ta tafi gida
  • Alkalin Kotun ya umarci su baiwa juna hakuri kana ya ɗage zaman ƙarar zuwa 30 ga watan Agusta

Kaduna - Wani Mutumi ɗan kimanin shekara 30, Muhammad Abdulganiyu, ya kai ƙarar Matarsa, Ma’arufat Ibrahim, gaban Kotun Shari'ar Musulunci da ke Magajin Gari a jihar Kaduna.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Matashin Magidancin ya maka matarsa a Kotun ne saboda ta tattara kayanta ta bar gidan su na aure ba tare da saninsa ba.

Kotun Shari'ar Musulunci.
Matar Aure Ta Gudu Daga Gidan Mijinta, Ta Ce Ba Zata Iya Zama da Yunwa Ba Hoto: dailytrust.com
Asali: Facebook

Muhammad ya shaida wa Kotun cewa ya dawo gida a ranar 16 ga watan Agusta, 2022 ya taras an sa makulli an garƙame kofar ɗaki kuma ya nemi matarsa sama da ƙasa bai ganta ba.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kakakin Majalisar Kaduna Ya Magantu Kan Shirin Tsige Gwamna El-Rufai

A jawabinsa ga Kotun, Magidancin ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Maƙocina ya gaya mun cewa mahaifiyar matata watau Suruka ta ce ta zo har gida ta tasa matata suka tafi. Ina son matata kuma ina biya mata bukatun ta."

Shin matar ta amsa laifinta?

A nata ɓangaren, matar auren, Ma'arufat, ta faɗa wa Kotun cewa ita ma tana son Mai gidanta amma ya zama tilas ta bar gidan saboda shi da kansa ya umarceta da ta tafi.

"Ina son mijina amma haka nan na tafi saboda ya faɗa mun zan iya tafiya domin babu abinci a gidan," inji Ma'arufat.

Ta kuma ƙara da bayanin cewa tana fama da ciwon 'Ulcer' wanda ake alaƙanta shi da yunwa kuma ga shi babu abinci a gida.

Alƙalin Kotun, Mai shari'a Malam Rilwanu Kyaudai, ya umarci ma'auratan su baiwa junan su haƙuri, sannan kuma ya ɗage zaman zuwa ranar 30 ga watan Agusta, 2022.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Yan Uwan Ɗan takarar Gwamna a Jihar Shugaban Ƙasa

A wani labarin kuma Dalilin Da Yasa Nake Hana Mijina Saduwa Da Ni, Matar Aure Ta Fada Wa Kotu

Wata Mata da ke neman a raba aurenta ta faɗa wa Kotu makasudin da yasa wasu lokutan take hana mijinta kwanciya da ita.

Matar ta kai karar mijin gaban Kotun kostumare da ke Ibadan, jihar Oyo ne saboda tace tana rayuwar baƙin ciki da 'ya'yanta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262