Jerin Kasashen 15 Afirka da Ke Fama da Hauhawar Farashin Abinci a 2022

Jerin Kasashen 15 Afirka da Ke Fama da Hauhawar Farashin Abinci a 2022

  • A shekarar nan, kasashen Afirka da yawa sun shiga matsanancin hali sakamakon hauhawar farashin kayayyaki da ya ninka na baya biyo bayan barkewar yakin Rasha da Ukraine
  • Bayan abinci, na daya daga cikin abubuwan da suka yi tashin gwauron zabi, lamarin da ya jefa jama'a da dama cikin tsananin yunwa da fatara
  • Kasashe irin su Najeriya sun shiga jerin wadanda suke fama da hauhawar farashin kayan abinci, kuma hakan ya taba darajar kudi da sauran fannonin tattalin arziki

A cewar wani rahoto daga jaridar Business Insider, lamarin hauhawar farashin kayayyaki a duniya ciki har da nan Najeriya da sauran kasashen Afirka, shi jawo tsadar rayuwa da al'umma ke ciki.

Yakin Rasha da Ukraine ne dalilin da kawo hauhawar farashin abinci, kasancewar kasashen biyu ne ke kan gaba wajen samar wadatacciyar alkama, sauran nau'ikan abinci da muhimman hatsi da ake amfani dasu yau da kullum.

Kara karanta wannan

An Yiwa Mawakin Najeriya, Eedris Abdulkareem Dashen Koda Cikin Nasara

Abu ne bayyananne inji rahoton cewa, hauhawar farashin abinci karuwa yake, kuma hakan da kassara tattalin arzikin aljifan gidaje da yawa a duniya.

Yadda kasashen Afrika ke fama da hauhuwar farashi
Jerin Kasashen 15 Afirka da ke fama da hauhawar farashin abinci a 2022 | Hoto: businessinsider.com
Asali: UGC

Deloitte ya ba da bayyanin cewa, gwabza yaki da ake tsakanin Rasha da Ukraine ya haifar da hauhawar farashin kayan abinci a duniya, kuma kasashe da dama na gab da shiga matsalar abinci nan ba da jimawa ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Tarin Kasashen Afirka, musamman Sudan da sauran kasashen a lardin na fama da fari da tashin hankalin da ya nakasa ainun ga fannin kudaden shigarsu da kuma jefa matalauta a kasar cikin tsananin yunwa.

A bangaren asusun ba da lamuni na duniya (IMF) rahotonsa na watan Yuli ya bayyana irin yanayin da nahiyar Afirka ka iya shiga, haka nan ya yi gargadin cewa tashin farashin kayan abinci.

Jerin kasashen da ke fama da hauhawar farashin kayan abinci

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yaudari manoma duk da kulla yarjejeniyar zaman lafiya, sun sace 16

  1. Zimbabwe: 309%
  2. Habasha: 35.5%
  3. Rwanda: 32.7%
  4. Ghana: 32.3%
  5. Malawi: 31.2%
  6. Burkina Faso: 28.9%
  7. Djibouti: 25.7%
  8. Angola: 25.1%
  9. Burundi: 24.4%
  10. Saliyo: kashi 23%
  11. Masar: 22.4%
  12. Najeriya: 22.02%
  13. Mozambique: 17.24%
  14. Senegal: 17.2%
  15. Somalia: 16.86%

Najeriya Na Bin Nijar, Benin, Togo Bashin N5.8bn Na Wutar Lantarki a 2020, Inji Wani Rahoto

A wani labarin, Najeriya na bin jamhuriyar Nijar, Benin da Togo kudaden da suka kai Naira biliyan 5.86 a shekarar 2020 na wutar lantarki da gwamnatin Najeriya ta nemi kasashen su biya.

A rahoton da Daily Trust ta fitar, an ce Najeriya a harkallar wutar lantarki da kasashen, ta nemi su biyu N16.31bn na wutar da ta ba su a shekarar ta 2023.

Rahoton na 2020 ya hukumar kula da wutar lantarkin Najeriya (NERC) ta fitar, an bayyana kafamonin kasashen guda uku da ke alhakin biyan wadannan kudaden kamar haka:

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

iiq_pixel