Abin Kunya: Rigima a Fili a Gidan ‘Yan Sanda a kan Sabon Daukar Aiki da Za ayi
- Sufeta Janar na ‘Yan Sanda na kasa zai sa kafar wando daya da Hukumar da ke kula da ayyukan ‘yan sanda a Najeriya watau PSC
- Hukumar PSC ta bada sanarwar za ta dauki sababbin kurata domin aikin ‘yan sanda, amma NPF tace babu wani shirin daukar aiki
- A madadin IGP Alkali Baba Usman, Olumuyiwa Adejobi yace al’umma su yi watsi da sanarwar domin ba ta da wata alaka da NPF
Abuja - Sufetan ‘Yan Sanda na kasa, Alkali Baba Usman yana rigima da hukumar PSC mai kula da aikin ‘yan sanda a dalilin shirin daukar aiki.
Rahoton Daily Trust na ranar Litinin, 22 ga watan Agusta 2022, ya bayyana cewa PSC ta bude shafin yanar gizo ga masu neman aikin ‘dan sanda.
Bayan hukumar ta bada sanarwar daukar aiki na shekarar nan ta 2022, sai rundunar ‘yan sanda ta bada sanarwar ayi watsi da maganar daukar aikin.
A wani jawabi da jami’in hulda da jama’a na ‘yan sandan Najeriya, CSP Olumuyiwa Adejobi ya fitar da jawabi yana cewa babu shirin daukar aiki.
Kamar yadda jawabin da CSP Adejobi ya shaida dazu a jawabin na sa, sanarwar PSC ba ta da alaka da daukar aikin rundunar ‘yan sanda na kasa.
Kakakin dakarun ya yi magana a Twitter, yana cewa babu abin da ya hada sanarwar da hukumar PSC ta fitar da shirin daukar aikin sababbin jami’ai.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta na sanar da jama’a cewa ba a soma fara daukar aikin kurata domin shiga aikin ‘yan sanda na shekarar 2022 ba.
Akasin sanarwar da aka wallafa a shafi na 21 na jaridar Daily Sun ta ranar Alhamis, 4 ga watan Agusta 2022 da hukumar ‘yan sanda ta PSC ta fitar.
Rundunar ‘yan sanda ta na shaida cewa wannan sanarwa ba ta da alaka da daukar aikin ‘yan sanda, kuma bai cikin shirin daukar sababbin dakaru.
Don haka ayi watsi da wannan kaco-kam. Shafin da aka bada ga masu neman aiki - http://www.recruitment.psc.gov.ng – bai da dangantaka da NPF.”
Asalin shafin jami'an NPF
A karshen jawabin, an yi kira ga masu sha’awar shiga ‘yan sanda da duk masu ruwa da tsaki su yi fatali da shafin yanar gizon, sannan biyewa irin sanarwar.
Ga masu bukatar bayani a kan aikin jami’an ‘yan sanda a Najeriya, CP Adejobi yace su bibiyi https://policerecruitment.gov.ng ko a https://www.npf.gov.ng.
EFCC ta manta da manyan kifaye
A yau aka ji labari shugaban Hukumar EFCC na kasa, Abdulrasheed Bawa yace sun je kotu da sama da mutum 970 kotu daga Junairu zuwa Satumban 2021.
Rahoto ya nuna mafi yawan wadanda ake shari’a da su, kananan masu laifi ne, EFCC ta manta da duk tsofaffin gwamnoni da-dama da ta soma bincikensu.
Asali: Legit.ng