Watanni 6: Jerin kudaden da gwamnatin Buhari ta kashe a kowane wata na tallafin man fetur
Wani rahoton TheCable ya ce, ya zuwa tsakiyar shekarar 2022, gwamnatin Najeriya ta ce kudaden da take kashewa a fannin tallafin man fetur ya haura kudaden shiga na harkar man fetur da gas na Najeriya da ya kai N210bn.
A cewar rahoton da jaridar Vanguard ta fitar, an ce gwamnatin Najeriya ta yi hasashen kashe akalla Naira tiriliyan 4 a shekarar ta 2022 na tallafin mai.
Jaridar ta ce tallafin man ya karu da 349.42% daga N350n a 2019 zuwa N1.573n na 2021. A shekarar 2020, an kashe N450bn a iya tallafin mai.
'Yan Najeriya da dama sun yi ta cece-kuce ganin yadda farashin mai ke kara hauhauwa ga kuma manyan kudade da gwamnatin Najeriya ke zubawa da sunan tallafi.
Jihohin Najeriya 10 Da Matansu Ke Kan Gaba Wurin Kwankwaɗar Barasa, Kamfanonin Giya Sun Samu N542bn Cikin Wata 6
A wannan rahoton, mun kawo muku adadin kudaden da gwamnati ta kashe cikin watanni shida kacal na 2020.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Rahoton ya TheCable ya ce an kashe akalla N1.59tr a cikin watanni shida na farkon 2022.
Ga dai kowane wata yadda aka kashe
- Watan Janairu: N210.38bn
- Watan Fabrairu N219.78bn
- Watan Maris: N245.77bn
- Watan Afrilu: N271bn
- Watan Mayu: N327.07bn
- Watan Yuni: N319.18bn
Ba a gama da 2022 ba, ga kuma batun 2023
Yayin da wannan na 2022 ne, wani hasashe ya nuna cewa, shekara mai zuwa za a fi kashe kudade masu yawan gaske.
Wani rahoton jaridar Daily Trust ya naqalto ministar kudi Zainab Ahmad na yin tsokaci game da adadin kudaden da Najeriya za ta kashe a 2023 da sunan tallafin man fetur.
A cewarta, gwamnatin Najeriya na hasashen kashe akalla N6.72tr domin tallafin man fetur.
Idan ba ku manta ba, gaba daya kasafin kudin Najeriya N17.127tr ne a 2022, inji Premium Times. Akwai yiwuwar ya karu a 2023, ga kuma tallafin man fetur kadai zai cinye sama da tiriliyan shida.
FG ta dakatar da shirin cire tallafin man fetur har sai baba ta gani
A wani labarin na can baya, gwamnatin tarayya ta dakatar da shirin cire tallafin man fetur har sai baba ta gani.
Kamar yadda TheCable ta ruwaito, gwamnatin ta shirya dakatar da biyan tallafi kan kayayyakin man fetur daga watan Yulin wannan shekarar.
Zainab Ahmed, ministar kudi, kasafi da tsarin kasa, ta sanar da hakan a wani taro da aka yi a majalisar dattawan kasar nan a Abuja a ranar Litinin, TheCable ta ruwaito hakan.
Asali: Legit.ng