Zahra Buhari Ta Taya Danuwanta Yusuf Da Matarsa Murnar Cika Shekara Daya Da Aure, Ta Saki Kyawawan Hotunansu
- Kamar wasa dan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Yusuf Buhari da matarsa kuma diyar sarkin Bichi, Zahra Nasiru Bayero sun shekara da aure
- Diyar Shugaban kasa, Zahra Buhari-Indimi ta je shafinta na soshiyal midiya domin taya danuwanta da kyakkyawar matarsa murnar zagayowar wannan rana
- A ranar 20 ga watan Agustan 2021 ne dai masarautar Bichi da ke jihar Kano ta kulla aure tsakanin Yusuf da Zahra Bayero
Najeriya - Shekara ta zagayo da shugaban kasa Muhammadu Buhari da mai martaba sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero suka zama surukai.
Diyar shugaban kasa, Zahra Buhari-Indimi ta taya dan’uwanta, Yusuf da matarsa Zahra Bayero murnar cika shekara daya da aure.
Yusuf Buhari da Zahra, diyar sarkin Bichi, Nasiru Ado Bayero, sun yi aure a ranar 20 ga watan Agustan 2021, a jihar Kano.
A wata wallafa da tayi a shafinta na Instagram a daren ranar Asabar, 20 ga watan Agusta, Zahra Indimi ta wallafa wani bidiyo dauke da hotunan ma’auratan sannan ta rubuta:
“Soyayyarku kyakkyawace matuka. Masha Allah.”
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ba’a Kyauta Mana Mu Talakawa: Rukayya Dawayya ta Koka Kan Yadda ‘Ya’yan Masu Kudi Ke Auran Junansu A Kasar
A wani labarin kuma, Shahararriyar jarumar Kannywood, Rukayya Umar Dawayya ta yi martani a kan yadda ake yin kwarya tabi kwarya wajen kulla auratayya a kasar nan.
Dawayya ta shawarci ‘ya’yan talakawa da ke da kyau a kan su daina yarda da soyayya tsakaninsu da yaran masu kudi domin magana ta gaskiya ba auransu za su yi ba.
A cewarta koda yaran na son su iyayensu ba za su amince a kawo masu diyar talakawa a matsayin suruka ba, don haka ta shawarce su da su tashi su nemi ilimi don gobensu.
Asali: Legit.ng