Bidiyon Yadda Wani Tsoho Mai Shekaru 66 da Ke Tallan Mangoro ke Nemawa Matarsa Kudin Magani
- Wani ma’aikacin jima’i dan kasar Ghana da ke sana’ar sayar da mangwaro don ciyar da kansa da matarsa da ba ta da lafiya ya nemi a taimaka masa.
- Isaac Antwi, mai shekaru 66, ya mallaki sana’ar matarsa ne bayan da ta yi rashin lafiya, kuma tun yanzu sama da shekara biyu yana sana’ar tasa.
- Dattijon na fuskantar korar shi daga dakinsa mai cike da rudani kuma yana rokon jama'a da su tallafa masa
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Accra, Ghana - Wani tsoho mai shekaru 66 dan kasar Ghana mai suna Isaac Antwi da ke tallan mangoro ya bayyana irin gwagwarmayar rayuwa da yake fama da ita, kana ga tsananin talauci.
Ya bayyana hakan ne a a wata hira da Crime Check TV GH, inda ya bayyana cewa ya kama sana'a ne tun lokacin da ya bar makaranta ya dukufa da neman kudi bayan rasuwar mahaifinsa.
Bayan Shekaru 16 da Aure, Magidanci Ya Fattaki Matarsa, Ya Aure Mai Gidan Haya Don Morar Hayar Kyauta
Antwi ya tuna cewa, a baya ya taba zuwa Najeriya ko zai samu canjin rayuwa, amma ya ga abubuwa kamar ana karawa wuta fetur. Daga baya ya sake dawowa Accra a kasar Ghana, nan ma dai babu abin da ya sauya.
Yana neman tamako
A cewar tsohon, ya kama sana'ar da matarsa ke yi sadda take lafiyayya bayan da ta kwanta rashin lafiya. Ga shi ba su da da bare jika, ga kuma tsananin talauci da nasassar mata, lamarin da ya kara cakude masa kenan.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Wannan tsoho dai mai suna Antwi na gab da fuskantar kora daga wani tarkataccen dakin da suke rayuwa, don haka ya bayyana cewa yana neman tallafi daga al'ummar da ke ganin za su iya taimaka masa.
Wanda ya tausaya ya ga kuma da halin taimakon wannan bawan Allah, to ga lambar Crime Check TV GH ta WhatsApp 0242074276 domin jin karin bayani game da shi.
Kalli bidiyonsa:
Yadda Wani Dan Acaba Ya Gamu da Mutumin Kirki, Ya Sauya Shi Zuwa ‘Celebrity'
A wani labarin, wani dan TikTok mai suna @alber_noir, ya yada wani gajeren bidiyo na yadda rayuwar wani dan acaba ta sauya daga cakwalkwali zuwa nasara.
Tun farin faifan bidiyon da aka yada a TikTok, mutumin ya bayyana cewa, shi dai abin da kawai yake dashi a rayuwa ba komai bane face fatan nasara.
A wani sashe na bidiyon kuwa, ya nuna shi fa a baya dan acaba ne, don haka ga ma babur din da yake tare kebura da ita.
Asali: Legit.ng