'Yan Bindiga Sun Kori Mutane Daga Garuruwa Takwas Na Jihar Kebbi
- Yan bindiga sun kai wani kazamin harin ƙauyuka Takwas a yankin ƙaramar hukumar Augie, jihar Kebbi
- Bayanai sun nuna cewa mafi yawan mazauna ƙauyukan sun bar gidajen su bayan kashe rayuka da sace wasu a harin ranar Laraba
- Hukumomin tsaro sun kai ɗauki yankunan ta hanyar ƙara yawan jami'an tsaro domin dakile faruwsr haka nan gaba
Kebbi - Aƙalla mutum uku aka tabbatar sun rasa rayukansu bayan wasu miyagun yan bindiga sun aikata mummunan ta'addanci a ƙauyen Zagi da wasu ƙauyuka a ƙaramar hukumar Augie, jihar Kebbi.
A ruwayar hukumar Dillancin labarai ta ƙasa (NAN), harin da yan bindigan suka kai ranar Laraba ya bar mutane da dama kwance a Asibiti suna karɓan magani, yayin da aka sace wasu 15.
Sauran ƙauyukan da mummunan harin ya shafa su ne, Tungar Rafi, Tungar Tudu, Keke, Kwaido, Sabon Garin Kwaido, Tungar Chichira da kuma ƙauyen Tattazai.
Jaridar The Cable ta ruwaito cewa mutanen da ke zaune a waɗan nan ƙauyukan su gudu daga gidajen su domin tsira daga ayyukan rashin imanin yan fashin daji.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Magajin garin Zagi, Muhammadu Lawali-Sule, ya ce maharan sun farmake su ne da tsakar dare kuma da farko mutane sun yi kokarin daƙile harin amma aka fi karfin su.
Wane mataki hukumomi suka ɗauka?
Kwamishinan yan sandan jihar Kebbi, Ahmed Magaji-Kontagora, ya ce tuni hukumarsa ta ƙara tura jami'an tsaro domin su tallafa wa waɗan da ke aiki a yankin.
Ya kuma tabbatar da cewa Sojojin Najeriya sun toshe yan bindiga daga sake samun damar kai hari nan gaba. Kwamishina ya shawarci mazauna da suka bar gidajen su da su koma, sannan su cigaba da harkokin su na yau da kullum.
Shugaban ƙaramar hukumar Augie, Lawal Muhammad, ya ce an ƙara girke jami'an tsaro a kewayen ƙauyukan.
"Ya zama wajibi mu yaba wa hukumomin tsaron mu bisa ƙara jibge jami'an tsaro a yankin da nufin dakile faruwar haka nan gaba. Sun ɗauki matakin da ya dace kuma harkoki sun daidaita."
A wani labarin kuma Luguden Wutan Sojoji Ya Hallaka Ƙasurguman Yan Ta'adda da Yawa a Yankuna Uku Na Arewa
Shugaban hukumar sojin saman Najeriya, Oladayo Amao, ya ce haɗin kan hukumomin tsaro ya haifar da gagarumar nasara.
A cewarsa, samamen da sojoji suka kai mafakar yan ta'adda ta sama da ƙasa a shiyyoyin arewa uku ya halaka manyan yan tada ƙayar baya.
Asali: Legit.ng