Mahaifiyar ’Ya’ya Hudu Ta Yada Kyawawan Hotunan Rusheshen Cikin da Jariranta Suka Zauna

Mahaifiyar ’Ya’ya Hudu Ta Yada Kyawawan Hotunan Rusheshen Cikin da Jariranta Suka Zauna

  • Wata uwar da ta haifi 'ya'ya hudu nan take ta yada wasu hotuna masu ban sha'awa na lokacin da take dauke da cikinsu
  • Matar da ta haifi har 'yan hudu kyawawa, an ganta cikin wani hoto mai daukar hankali lokacin da take da juna biyu
  • Ba a bar jama'ar soshiyal midiya a baya ba, sun tofa albakacin bakinsu, wasu matan kuma har fata suke su haifi 'yan hudu

Hotunan wata dauke da rusheshen ciki ya ba jama'a da dama mamaki tare jawo cece-kuce a kafar sada zumunta

A shekaru baya kadan da suka wuce, kyakkyawar matar ta haifi 'yan hudu da ta lakaba ma suna Camille, Casper, Carissa, da Casen.

Ta jawo cece-kuce a kafafen sada zumunta lokacin da ta yada hotunan 'ya'yanta lafiyayyu da ta haifa a lokaci guda, wasu kuma suka nemi ganin wani irin rusheshen ciki ne 'ya'yan suka zauna a ciki.

Kara karanta wannan

Dalilin Da Yasa Nake Hana Mijina Damar Saduwa da Ni, Matar Aure Ta Faɗa Wa Kotu

Yadda wata mata ta haifi 'yan hudu, ta yada hotunan rusheshen cikinta
Mahaifiyar 'ya'ya hudu ta yada kyawawan hotunan rusheshen cikin da jariranta suka zauna | Hoto: @thequadruplet_c4
Asali: UGC

Bayan wani dan lokaci, ta yada wasu sabbin jerangiyar hotunanta a intanet, inda ta nuna 'ya'yan nata da kuma lokacin da take da juna biyu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kalli hotunan:

'Yan soshiyal midiya sun shiga ta'ajibi

@cindyama3 tace:

"Ina roka wa kaina irin wannan albarkar."

@babynanasmum ta yi martani tare da yabawa mijin matar, ta ce:

"Wannan abu ne mai kyau, Allah ya yi maka albarka da har ka tsaya mata har zuwa wannan lokacin."

@akyuahberries ta ce:

"Ina taya ki murna 'yar uwa. Ina neman tabarrukinki."

@official_mss ta ce:

"Ina neman irin wannan albarka ta 'yan hudu. Ta yaya ake samu don Allah?"

@queenmandy462 ta ce:

"Ina yi ma kaina fatan irin wannan albarkar mai ban mamaki daga wurin Allah. Zan karbi taya murnarki, ranki ya dadi."

@mizz_gh ta ce:

"Ina tsammanin 'yan biyu, ashe ya haura haka, abin mamaki. Allah ya yi muku albarka ya kuma kare ku daga sharri, ina taya ku farin ciki."

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun ceto mutum 4 daga hannun miyagun 'yan bindiga a wata jiha

@princessjay404 ta ce:

"Ahhh, Allah kenan, wannan aikin sai kai din. Mun gode Allah kin sauka lafiya. Ina taya ki murna."

Uba ya tsere yayinda matarsa ta haifi yan hudu a Edo

A wani labarin, wani uban yara biyar ya tsere bayan matarsa ta haifi yara hudu zur a ranar Asabar, 2 ga watan Janairu a Benin, babbar birnin jihar Edo.

Wata mai amfani da shafin Facebook mai suna Sarah Az Izevbigi ce ta bayyana hakan. A cewar matar, mai jegon mai suna Rita Ndibisu, na bukatar taimakon yan Najeriya don kula da yaranta.

Ta roki yan Najeriya da su taimaki Rita da yaranta yayinda ta wallafa asusun bankin da za a sa kudin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel