Sojoji Sun Kai Samame Sansanin Rikakken 'Dan Bindiga Lawal Kwalba, Sun Kwato Kayan Hada Bama-bamai
- Jami'an tsaro a jihar Kaduna sun kai samame sansanin rikakken 'dan bindiga Lawal Kwalba a dajin Chikun dake jihar Kaduna
- An samo buhuna 27 na taki tare da batira wadanda ake kyautata zaton hada bama-bamai suke yi da su ganin alakarsu da 'yan ta'adda
- Kamar yadda Samuel Aruwan ya sanar, an samo babur tare da wayoyin salula biyu sannan an cafke wasu da ake zargi
Kaduna - Jami'an tsaro a jihar Kaduna a ranar Alhamis sun kai samame maboyar rikakken 'dan bindiga Lawan Kwalba a karamar hukumar Chikun ta jihar inda suka samo kayayyakin hada bama-bamai.
Kwamishinan tsaron cikin gida, Samuel Aruwan, yace jami'an tsaron sun samo buhunan taki 27 wadanda ake amfani da su wurin hada abubuwa masu fashewa a cikin dajin Chikun, Channels Tv ta rahoto.
Aruwan yace, dakarun sun kakkabe sansanin Kwalba dake Fadin Dawa a yankin Dende na karamar hukumar.
Jami'in gwamnatin yace jami'an tsaron na matukar kokari kan yadda suka zage-damtse wurin yaki da ta'addanci a jihar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Premium Times ta rahoto cewa, yace a bayanai da gwamnatin jihar ke samu, dakarun Operation Forest Sanity sun yi aikin ne bayan samun bayanan sirri.
"Dakarun sun kai farmaki har sansanin inda suka samo batira da buhunan taki 27. Wadannan kayayyakin alamu na nuna cewa ana hada abubuwa masu fashewa ne da su ganin yadda 'yan bindigan ke samun hadaka da 'yan ta'adda.
"Har ila yau, an samo babur daya da wayoyi biyu yayin da 'yan bindigan suka ranta a na kare kafin isar dakarun sojin.
"Sojojin basu tsaya nan ba, sun sake tsananta bincikensu har zuwa harabar sansanin kuma sun kama wasu. Ana cigaba da bincike kan wadanda aka kama a halin yanzu.
"Gwamnatin jihar Kaduna ta karba rahoton da gamsuwa kuma da yabawa kokarin sojojin wurin aikin da suke yi," Aruwan yace.
Kaduna: Dakarun Soji Sun yi Arangama da 'Yan Bindiga, Sun Kwato Mai Jego Da Jaririnta
A wani labari na daban, gwamnatin jihar Kaduna tace hukumomi sun ceto wata mai jego da wasu mutum biyu a wuraren Ungwan Namama, a kan babban hanyar Zaria zuwa Kano, jaridar The Cable ta ruwaito.
Samuel Aruwan, kwamishinan tsaron cikin gida na jihar, a wata takardar da ya fitar ranar Alhamis, yace dakarun sun ci karo da 'yan bindigan dake hijira a yankin kuma suka yi musu ruwan wuta, lamarin da ya tirsasa su barin mutum uku da suka sato sannan suka tsere.
Asali: Legit.ng