Budurwa ta Kaiwa Saurayi Ziyara, ya Fadi ya Mutu a Bandakin Otal, SP Benjamin Hundeyin

Budurwa ta Kaiwa Saurayi Ziyara, ya Fadi ya Mutu a Bandakin Otal, SP Benjamin Hundeyin

  • Azal ta fadawa wata budurwa yayin da ta kai wa wani mutumi ziyara har jihar Legas a dakin otal bayan haduwarsu a yanar gizo
  • Kamar yadda SP Benjamin Hundeyin ya bayyana, mutumin ya kama hanyar zuwa bandaki amma ya yanke jiki ya fadi ya mutu har lahira a otal din
  • Budurwar ta dinga rokon 'yan sanda da su taimaka kada su sanar da iyayenta, duk da zarginta ake yi da kisan kai

Legas - Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Legas, SP Benjamin Hundeyin, ya ja kunne jama'a da su kiyayi kai wa wadanda basu sani ba ziyara ba tare da sun sanar da kowa ba.

Ya bayyana wannan shawarar ne a wallafar da yayi a shafinsa na Twitter a ranar Lahadi da yammaci.

Kara karanta wannan

Bidiyon Budurwa da Wani Sabon Salon Kitso mai Bada Mamaki Ya Janyo Cece-kuce

SP Benjamin
Budurwa ta Kaiwa Saurayi Ziyara, ya Fadi ya Mutu a Bandakin Otal, SP Benjamin Hundeyin. Hoto daga @BenHundeyin
Asali: Twitter

Kamar yadda Hundeyin ya sanar, wata matashiyar budurwa ta je har Legas domin haduwa da wani mutumi da ta hadu da shi a yanar gizo.

Rashin sa'a da tsautsayin a yi, ya saka ta cikin matsala inda mutumin ya yanke jiki ya fadi ya mutu a bandakin dakin otal din da ya kama musu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kamar yadda wallafar tace:

"Ku guji kai ziyara babu sanin kowa ga mutanen da baku sani ba. Wata budurwa ta tafi har Legas domin ganawa da mutumin da suka hadu a yanar gizo.
"A dakin otal din, mutumin ya tafi bandaki inda ya yanke jiki ya fadi tare da mutuwa. Budurwar tana rokon kada a sanar da iyayenta. Zargin kisan kai? A kiyaye."

Jama'a sun yi martani

Wannan wallafara ta dauka hankalin jama'a inda suka dinga martani a kai. Ga wasu daga cikin martanin da Legit,ng ta tattaro muku:

Kara karanta wannan

Rikici Ya Barke Tsakanin Kungiyar Yarbawa Na OPC Da Dillalan Shanu A Jihar Kwara

@trending_meid yace:

"Ta yaya wannan ya zama laifin budurwar, a kan mene za a sanar da iyayenta tunda ba yarinya bace.?

@adlanheman yace:

"Daga karshe ta shiga matsala bayan jan kunne da tarbiya daga iyaye."

@kazhamza yace:

"Ku yi gwajin gane abinda ya kashe shi kafin ku kama budurwar ku kuma bayyanata ga manema labarai."

@ekenwaezianowai yace:

"Abun kunya ne har da kake yanke hukuncin cewa kisan kai ne bayan ko bincike baku gama ba. Me ake koyar da ku a makarantar 'yan sanda?"

Asali: Legit.ng

Online view pixel