Ma’aikatan Muhalli a Abuja Sun Yi Barazanar Rufe Makabarta a Kewayen Birnin Tarayya
- Ma'aikatan muhalli a babban birnin tarayya sun bayyana barazanar rufe dukkan makabartu a birnin
- Kungiyar ma'aikatan muhalli sun koka ga yadda hukumomi suka gaza aiwatar da sabon tsarin albashi ga ma'aikata
- Ma'aikata a Najeriya na yawan nuna damuwa ga irin kudaden da suke samu na albashi bisa la'akari da tattalin arziki
FCT, Abuja - Ma’aikatan muhalli a babban birnin tarayya Abuja, sun yi barazanar rufe dukkan makabartu a Abuja saboda wasu dalilai, Daily Trust ta ruwaito.
Ma’aikatan, wadanda suka kulle makabartar Gudu a babban birnin kasar, sun mika wuya ga matsin lamba daga fadar shugaban kasa, kuma sun bude filin a safiyar ranar Alhamis.
Ma’aikatan da suka fusata sun danganta matakin rufe makabartar ne da gazawar hukumar babban birnin tarayya Abuja wajen aiwatar da sabon tsarin albashi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwamared Muktar Bala, shugaban kungiyar ma’aikata karkashin AUPCTRE na kungiyar AEPB, ya ce duk da cewa kungiyar ta amince da bude wasu makabartun, amma za ta rufe dukkan makabartun idan ba aiwatar da abin da suke bukata ba.
Bala, wanda ya nuna damuwarsa kan rashin tsari a hukumar wajen kula da jin dadin mambobin kungiyar, ya ce sun fuskanci matsalolin lafiya da dama a yayin da suke kula da gawarwakin da aka yi watsi da su.
Jaridar Tribune Online ta rahoto Kwamared na cewa:
"Mutane suna tunanin harkar shara ne kawai muke yi. Ba su san cewa ko gawarwakin da ba a gano 'yan uwansu ba a asibitoci mu ne ke kula da su ba.
“Wadannan gawawwakin da suka wuce shekaru 3 zuwa 4 suna kwance a asibiti, muna kula da su, ba tare da sanin me ya kashe su ba.
“Asibitoci na zuwa wurinmu a lokacin da suke son a yi jana’iza mai yawa ga irin wadannan gawawwakin.
"Idan akwai gawarwakin da ba gano masu su ba ko gawarwakin da ba gano ba da aka tsinta kan hanya ko kuma a wasu wurare, ‘yan sanda za su rubuta rahoto su kawo mana don mu binne su.
“Duk wadannan hadurran, mutane ba sa kallon cewa muna yin wani abu. Muna so mu gaya wa gwamnati cewa baya ga kula da shara, muna yin wasu abubuwan."
Kada Ku Zabi Dan Siyasar Da ’Ya’yansa Ke Karatu a Waje, Inji Shugaban ASUU
A wani labarin, shugaban kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) Farfesa Emmanuel Osodeke, a ranar Laraba shawarci daliban Najeriya kada su zabi ‘yan siyasar da ‘ya’yansu ke karatu a makarantun kasashen waje, Punch ta ruwaito.
Osodeke ya yi magana ne a shafin Twitter Space Webinar, wanda Premium Times ta shirya mai taken,‘ASUU strike, Revitalisation Fund and the Way Forward’ don nemo mafita ga mafitan yajin ASUU.
Da yake magana kan wasu hanyoyin ci gaba na mafita ga yajin aikin, ya ce kada dalibai su zabi ‘yan siyasar da ba za su wakilci muradunsu ba.
Asali: Legit.ng