Yajin Aikin Ma'aikatan Wutar Lantarki: NUEE ta Garkame Ofishin TCN na Kaduna

Yajin Aikin Ma'aikatan Wutar Lantarki: NUEE ta Garkame Ofishin TCN na Kaduna

  • Kungiyar ma'aikatan wutar lantarki ta kasa sun dira ofishin rarrabe wutar lantarkin na shiyyar Kaduna inda suka dakile dukkan ayyuka
  • Basu tsaya nan ba, sun saka makullansu inda suka garkame ofishin rarrabe wutar lantarkin bayan ma'aikatan sun bar farfajiyar ofishin
  • Ma'aikatan Kungiyar NUEE sun fada yajin aikin sakamakon wasu bukatu nasu da suke son gwamnatin tarayya ta cika musu

Kaduna - Mambobin Kungiyar ma'aikatan wutar lantarki sun fada yajin a hedkwatar su ta Kamfanin Rarrabe Wutar Lantarki na Kaduna, bisa ga umarnin shugabannin kungiyar ta kasa.

Channels TV ta rahoto cewa, Kamfanin Rarrabe Wutar Lantarki na shiyyar Kaduna shi ke samar wa jihohin arewa maso yammaci kamar Kaduna, Kebbi, Sokoto da Zamfara da wutar lantarki.

Kungiyar NUEE
Yajin Aikin Ma'aikatan Wutar Lantarki: NUEE ta Garkame Ofishin TCN na Kaduna. Hoto daga leadership.ng
Asali: UGC

A safiyar Laraba, jami'an NUEE sun dira ofishin Rarrabe Wutar Lantarki na Kaduna dake Mando inda suka rufe dukkan ayyuka, hakan yasa dole ma'aikatan suka bar farfajiyar kamfanin kuma suka saka makullansu tare da garkame wurin.

Kara karanta wannan

Borno: Shugaba Buhari Zai Tafi Maiduguri, Zai Kaddamar da Ayyukan Zulum da Tallafa Wa Talakawa

Sun sha alwashin cewa, ba zasu koma yajin aikin ba har sai gwamnatin tarayya ta cika musu bukatunsu, jaridar The Cable ta ruwaito.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kungiyar ma'aikatan wutar lantarkin suna yajin aikin ne kan rike musu wasu kudade da tsohuwar hukumar PHCN tayi, dakatar da sharuddan aiki da kuma umarnin hukumar TCN na yin jarabawar karin girma ga mukaddasan manajoji zuwa mataimakan manajoji.

Ku Nemi Taimakon Ubangiji Kan Al'amuran Siyasarmu, IBB Ga 'Yan Najeriya

A wani labari na daban, Ibrahim Babangida, tsohon shugaban kasar Najeriya na mulkin soja, yace 'yan Najeriya su nemi taimakon Ubangiji kan alkiblar da zasu dosa a al'amuran siyasar kasar nan.

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa, Babangida ya sanar da hakan ne a ranar Talata yayin zantawa da manema labarai a Minna, babban birnin jihar Niger domin tunawa da zagayowar ranar haihuwarsa.

Kara karanta wannan

Jerin Manyan Mukamai 15 Masu Gwabi Da El-Rufai Da APC Ta Arewa Maso Yamma Suka Nema Daga Wurin Tinubu

Tsohon shugaban kasan ya cika shekaru 81 a ranar 17 ga watan Augustan 2022.

A jawabinsa, yayi kira ga 'yan Najeriya da su cigaba da yin imani wurin hadin kan kasar nan tare da mayar da hankali da sa ran cewa komai zai daidaita.

Asali: Legit.ng

Online view pixel