Shugaba Buhari Ya Dira Birnin Maiduguri Jihar Borno, Zai Kaddamar da Ayyuka
- Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya sauka a Maiduguri, babban birnin jihar Borno a wata ziyara ta kwana ɗaya
- A wannan ziyara da ta kasance ta uku cikin shekara ɗaya, Buhari zai kaddamar da muhimman ayyukan cigaba
- Haka nan, Buhari zai kaddamar da ranar tallafa wa marasa galihu ta duniya ƙarƙashin ma'aikatar jin kai da walwala
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Borno - Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya dira birnin Maiduguri, babban birnin jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya a wata ziyarar aiki da ya fara.
Yayin wannan ziyara da shugaban ya kai jihar Borno yau Alhamis 18 ga watan Agusta, 2022, ana sa ran zai kaddamar da ranar jin ƙan marasa ƙarfi ta duniya, kamar yadda Leadership ta ruwaito a shafinta na tuwita.
Daily Trust ta rahoto cewa Jirgin shugaban ƙasan ya sauka a ɓangaren rundunar sojojin sama da ke Babban Filin jirgin sama na ƙasa da ƙasa a Maiduguri da misalin ƙarfe 12:15 na rana.
Ana tsammanin shugaban ƙasan zai kaddamar da wasu ayyukan cigaba da gwamnatin Borno karkashin jagorancin gwamna Farfesa Babagana Umaru Zulum, ta zuba wa al'ummarta.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Hotunan Ziyarar Buhari
Manyan mutanen da suka tarbi Buhari
Shugaba Buhari ya samu kyakkyawar tarba daga gwamna Babagana Umaru Zulum, mataimakinsa, Usman Kadafur, ministar walwala da harkokin jin ƙai, Sadiya Umar Farouk.
Sauran waɗanda suka je tarban Buhari sun haɗa da ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, yan majalisun tarayya da na jiha da sauran kusoshin gwamnati.
Daga nan, kai tsaye shugaban ƙasan ya zarce zuwa wurin da zai kaddamar da ayyukan, waɗan da suka haɗa da Anguwar gidajen Malamai, da wasu gidaje da gwamnati ta gina a Molai.
A wani labarin kuma Rabiu Musa Kwankwaso ne zai gaji kujerar shugaban ƙasa Buhari a 2023 inji Buba Galadima
Buba Galadima, babban jigon jam'iyya mai kayan marmari ya yi hasashen Kwankwaso zai lashe zaɓen shugaban kasa a 2023.
Tsohon makusancin shugaba Buhari ya bayyana yadda tsohon gwamnan Kano zai yi nasara a jihohin ƙasar nan.
Asali: Legit.ng