Gwamna Matawalle Ya Kubutar da Jami'in Hukumar Yan Sanda Daga Hannun Yan Bindiga

Gwamna Matawalle Ya Kubutar da Jami'in Hukumar Yan Sanda Daga Hannun Yan Bindiga

  • Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya yi nasarar ceto DSP Usman Ali, daga hannun yan bindiga
  • Yan Fashin daji da ake zaton masu garkuwa ne sun sace jami'in ɗan sandan a kan titin Gusau zuwa Ɗansadau ranar 12 ga watan Agusta
  • Jami'an tsaron da gwamnatin Matawalle ta kafa sun kubutar da shi tare da gabatar wa gwamnan, wanda ya nuna jin daɗinsa

Zamfara - Gwamna Muhammad Bello Matawalle na jihar Zamfara, a ranar Laraba ya kuɓutar da, DSP Usman Ali, jami'in ɗan sanda mai kula da Caji Ofis ɗin Magami da ke Gusau daga hannun masu garkuwa.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da Sakataren watsa labarai ga gwamna, Jamilu Birnin-Magaji, ya fitar.

Kara karanta wannan

Na Yi Alkawarin Kuɗi N50,000 Ga Duk Wanda Ya Fallasa Bayanan Yan Bindiga a Jihata, Gwamnan APC

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle.
Gwamna Matawalle Ya Kubutar da Jami'in Hukumar Yan Sanda Daga Hannun Yan Bindiga Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Yan fashin daji da ake zargin masu garkuwa ne sun yi awon gaba da DSP Ali a kan titin Gusau-Dansadau ranar 12 ga watan Agusta, 2022.

Sai dai a halin yanzun, mai girma gwamna ya ceto ɗan sanda ta hanyar namijin kokarin jami'an tsaron gwamnatin jiha, waɗan da suka damƙa wa gwamnan shi a gidan gwamnati da ke Gusau, ba tare da ya cutu ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Matawalle ya yaba da sabbin matakai

Gwamna Matawalle, lokacin da ya karɓi babban jami'in, ya nuna gamsuwarsa da matakan da gwamnatinsa ta ɗauka da nufin kawo ƙarshen ayyukan ta'addancin yan bindiga da masu garkuwa da mutane.

Ya taya ɗan sandan murna bisa samun yanci daga hannun yan ta'adda kana ya yi Addu'a Allah ya shige gaba, ya kawo wa al'umma karshen ayyukan yan bindiga da sauran manyan laifuka.

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa Ta Ɓullo a PDP, Taron Sasanta Atiku Abubakar da Gwamna Wike Ya Gamu da Cikas

DSP Ali ya nuna jin daɗinsa, ya kuma gode wa gwamnan da sauran waɗan da suka ba da gudummuwa har Allah ya taimaka ya samu yanci daga sansanin yan bindiga, Rahoton Sun News ya tabbatar.

A wani labarin kuma Sojoji sun hallaka manyan Hatsabiban yan Ta'adda da dama a yankuna Uku na Arewa

Shugaban hukumar sojin saman Najeriya, Oladayo Amao, ya ce haɗin kan hukumomin tsaro ya haifar da gagarumar nasara.

A cewarsa, samamen da sojoji suka kai mafakar yan ta'adda ta sama da ƙasa a shiyyoyin arewa uku ya halaka manyan yan tada ƙayar baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel