Dubun Wani Mutumi Ta Cika, An Kama Shi Da Bindigu Zai Kaisu Kano
- Yan banga sun yi ram da wani mutumi ɗauke da bingidu da dama zai ba da sako a kai su Kano a tashar motocin Zuba, birnin tarayya Abuja
- Kwamandan yan Bangan, Yahaya Madaki, ya ce mutumin bai so aka buɗe kayan sakon ba, tuni yan sanda suka kama shi
- Hukumar yan sanda ta bakin mai magana da yawunta, DSP Josephine Adeh, ta ce zata gudanar da bincike
Abuja - Tawagar ƴan Banga da ke aikin tsaro a Tashar Motoci a Zuba, babban birnin tarayya Abuja, sun cafke wani mutumi ɗauke da Bindigu Takwas yana shirin kai su Kano.
Kwamandan Yan bangan yankin, Yahaya Madaki, wanda ya tabbatar da lamarin ga jaridar Daily Trust Jiya Laraba, ya ce mutumin ya tsaya a bakin Titi kusa da Gidan mai da aka fi sani da Ɗan Kogi da ƙarfe 2:00 na rana.
A cewar kwamandan, bayan ya tsaya a wurin, mutumin da ake zargin ya fara kokarin neman Motar da zata je Kano.
Shugaban yan bangan ya ce:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Da aka gabatar masa da Direban da ke lodi a lokacin, sai mutumin ya damƙa masa wani ƙunshin kayayyaki tare da lambar wayar wanda zai zo ya karɓi kayan a Kano. An nemi ya biya N10,000 na aikin kuma nan take ya biya."
"Bayan haka ne Direban ya nemi a buɗe kunshin don tabbatar da abun da ke ciki amma mutumin ya ce ba bukata, ana cikin haka ne ya yi kokarin guduwa amma mutane suka zagaye shi."
Me aka gano a cikin kayan?
Kwamandan Yan Bangan ya kara da cewa da suka buɗe katan ɗin kayan sun ci karo da bindigun AK-47 guda Biyar da kuma wasu Bindigu a ciki.
Bayanai sun nuna cewa DPO yan sanda mai kula da Caji Ofis din Zuba, CSP Osor Moses, da kansa ya jagoranci tawagar dakaru zuwa wurin kuma suka yi ram da mutumin.
Da aka nemi jin ta bakin DPO na Zuba ya umarci wakilin jaridar ya tuntubi hukumar yan sanda ta birnin tarayya Abuja.
Sai dai a bangarenta, Mai magana da yawun hukumar yan sandan Abuja, DSP Josephine Adeh, ta yi alƙawarin gudanar da bincike sannan ta dawo ga manema labarai.
A wani labarin kuma Gwamnan Zamfaraa ya ceto wani babban jami'in Ɗan sanda daga hannun ƴan Bindiga
Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya yi nasarar ceto DSP Usman Ali, daga hannun yan bindiga.
Yan Fashin daji da ake zaton masu garkuwa ne sun sace jami'in ɗan sandan a kan titin Gusau zuwa Ɗansadau ranar 12 ga watan Agusta.
Asali: Legit.ng