Dakarun Sojoji Sun Kai Samame Sansanin Yan Ta'adda A Kaduna, Sun Ceto Mata 6

Dakarun Sojoji Sun Kai Samame Sansanin Yan Ta'adda A Kaduna, Sun Ceto Mata 6

  • Dakarun tsaro na Operation Forest Sanity a Kaduna sun yi nasarar kai wa yan bindiga samame a sansaninsu a karamar hukumar Chikun
  • Samuel Aruwan, Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida ya sanar da hakan inda ya ce jami'an tsaron sun ceto mutane shida da yan bindigan ke tsare da su
  • Aruwan ya kuma mika godiyar gwamnatin jihar Kaduna ga shugabannin rundunar sojojin Najeriya da hukumar DSS da sauran hukumomin tsaro da suka taimaka a atisayen

Jihar Kaduna - Dakarun 'Operation Forest Sanity' a ranar Talata sun kai samame sansanin yan bindiga da ke garuruwan Kuriga da Maina a karamar hukumar Chikun inda suka ceto mutane shida.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na Jihar, Samuel Aruwan ne ya sanar da hakan cikin wata kunshin sanarwar da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Kaduna: Dakarun Soji Sun yi Arangama da 'Yan Bindiga, Sun Kwato Mai Jego Da Jaririnta

Wadanda aka ceto daga hannun yan bindiga.
Dakarun Sojoji Sun Kai Samame Sansanin Yan Ta'adda A Kaduna, Sun Ceto Mata 6. Hoto: Samuel Aruwan.
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wadanda aka ceto daga hannun yan bindiga.
Dakarun Sojoji Sun Kai Samame Sansanin Yan Ta'adda A Kaduna, Sun Ceto Mata 6. Hoto: Samuel Aruwan.
Asali: Facebook

Aruwan ya ce wadanda aka ceto din sun hada da Sahura Hamisu, Ramlatu Umar, Saudatu Ibrahim, Maryam Shittu, Fatima Shuaibu da Khadijah Mohammed (tare da jinjirarta).

Kwamishinan ya ce rundunar sojin wacce ta sanar da gwamnatin jihar cigaban ta ce tuni an sada wadanda aka ceto da iyalansu.

Ya ce "Bayan nasarar da jami'an tsaron suka samu a karshen mako sun cigaba da kai sumame sansanin yan bindiga a jihar.
"Yayin wani rahoto na aikin jami'an tsaro da gwamnatin Kaduna ta samu, dakarun Operation Forest Sanity a safiyar ranar Talata sun kai samame, sun ceto mutane shida a garuruwan Kuriga da Manini a karamar hukumar Chikun.
"A cewar rahoton, sojojin sun yi karo da wadanda ake zargin yan bindigan ne kuma suka fatattake su. Bayan lalata sansanin sun ceto mutane shida da ake tsare da su a wurin."

Kara karanta wannan

Mazauna a Kaduna sun fusata, sun sheke wata wata mai boye 'yan bindiga a gidanta

Ya cigaba da cewa gwamnatin jihar Kaduna ta mika godiyar ga dukkan jami'an tsaron bisa nasarar.

Hakazalika, ta mika godiya na musamman ga babban hafsan tsaro, babban hafsan sojojin ƙasa, babban hafsan sojojin sama da GOC 1 na rundunar sojojin Najeriya da hukumar DSS bisa atisayen da ake kaiwa sansanin bata garin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel