Ana Taron Gwamnoni a Aso Rock Don Magance Matsalar Tsaro da Tattalin Arziki Buhari Bai Halarta Ba

Ana Taron Gwamnoni a Aso Rock Don Magance Matsalar Tsaro da Tattalin Arziki Buhari Bai Halarta Ba

  • Rahoton da ke iso mu ya bayyana cewa, a halin yanzu gwamnonin Najeriya sun shiga ganawa a fadar Buhari
  • An ruwaito cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari bai halarci taron ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton
  • Rahoton da muka samo ya bayyana gwamnonin da suka halarta da kuma wadanda suka turo wakilai

Aso Rock, Abuja - A halin yanzu dai mambobin kungiyar gwamnonin Najeriya na cikin taro a dakin taro na banquet da ke fadar shugaban kasa, Aso Rock, Abuja.

Gwamnonin dai na ganawa ne kan halin da tattalin arzikin kasar nan ke ciki, rashin tsaro, da kiwon lafiya da dai sauransu, rahoton Punch.

A cewar wata sanarwa da Daraktan yada labarai da hulda da jama’a na kungiyar, Abdulrazaq Bello-Barkindo ya sanyawa hannu a ranar Talata, ya ce yanayin tattalin arzikin Najeriya da tsaro ne za su kasance kan gaba a ganawar.

Kara karanta wannan

Zan gyara fannin ilimi cikin wata shida idan na gaji Buhari, inji wani dan takara

Gwamnonin Najeriya sun shga ganawa kan lamarin tsaro da tattalin arziki
Ana Taron Gwamnoni a Aso Rock Don Magance Matsalar Tsaro da Tattalin Arziki Buhari Bai Halarta Ba | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Taron ya zo ne makwanni bayan gwamnonin sun ba da shawarwari 33 ga shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya), don ya aiwatar a ceto tattalin arzikin kasar nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Barkindo ya bayyana cewa kungiyar ta NGF ta damu da halin kuncin tattalin arzikin da Najeriya ke ciki, ga kuma irin yanayin talauci da ‘yan Najeriya ke fama dashi a karkashin gwamnatin Buhari.

A cewar sanarwar:

“Gwamnoni da dama sun yi tunanin cewa lokaci ya yi da za a gaya wa juna gaskiya ta hanyar fuskantar juna a kan lamarin da kuma yin tunani a kai."

Wadanda suka halarci taron

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoton, akalla gwamnoni 25 ne suka halarci taron, wasu kuma mataimakansu ne suka wakilce su.

Daga cikin gwamnonin sun hada da Kayode Fayemi na Ekiti, Babagana Zulum na Borno, Bala Mohammed na Bauchi, Godwin Obaseki na Edo, Inuwa Yahaya na Gombe da Abubakar Badaru na Jigawa.

Kara karanta wannan

Karfin hali: Dalibin kwaleji ya yI barazanar sace 'Provost', ya shiga hannun hukuma

Hakazalika da Simon Lalong na Plateau, Dapo Abiodun na Ogun, Babajide Sanwo-Olu na Legas. , Rotimi Akeredolu na Ondo, AbdulRahman AbdulRazaq na Kwara, Hope Uzodinma na Imo, Aminu Tambuwal na Sokoto, Dave Umahi na Ebonyi da Gboyega Oyetola na Osun.

Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da Mataimakin Gwamnan Kogi, Edward Onoja, Adebayo Lawal na Oyo, Moses Ekpo na Akwa Ibom, Cecilia Ezeilo na Enugu da Lawrence Ewhrudjakpo na Bayelsa.

A halin da ake ciki dai ba a ga shugaba Buhari a taron ba.

Ku Nemi Taimakon Ubangiji Kan Al'amuran Siyasarmu, IBB Ga 'Yan Najeriya

A wani labarin, Ibrahim Babangida, tsohon shugaban kasar Najeriya na mulkin soja, yace 'yan Najeriya su nemi taimakon Ubangiji kan alkiblar da zasu dosa a al'amuran siyasar kasar nan.

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa, Babangida ya sanar da hakan ne a ranar Talata yayin zantawa da manema labarai a Minna, babban birnin jihar Niger domin tunawa da zagayowar ranar haihuwarsa.

Kara karanta wannan

Shawari kyauta: Hanyoyi 15 da za ku bi domin kiyaye kanku daga fadawa matsala a Najeriya

Tsohon shugaban kasan ya cika shekaru 81 a ranar 17 ga watan Augustan 2022. A jawabinsa, yayi kira ga 'yan Najeriya da su cigaba da yin imani wurin hadin kan kasar nan tare da mayar da hankali da sa ran cewa komai zai daidaita.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.