Yadda Wani Dalibin Kwalejin da Ya Yi Barazanar Sace ‘Provost’ Dinsu, Ya Shiga Hannu
- Jami'an hukumar NSCDC sun yi nasarar kame wani matashin da ya lallaba, ya yi barazanar sace shugaban makarantarsu
- An gurfanar da dalibin kwalejin jihar Neja a gaban kotu bisa zarginsa da aikata wasu munanan laifuka biyu
- Ya zuwa yanzu, ana ci gaba da neman wanda suka hada baki tare suka nemi shugaban makarantar ya basu kudi
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
New Bussa, jihar Neja - A jihar Neja, wani dalibi ya ba da mamaki yayin da ya tura wasikar baranza ga shugaban kwalejin da yake karatu da sunan yunkurin sace shi.
Jami'an Hukumar tsaron Najeriya ta NSCDC, ba su yi kasa a gwiwa ba, sun yi nasar kwamushe wannan matashi mai shekara 18.
Rundunar ta ce ta kama ne bisa zargin yunkurin yin garkuwa da shugaban Kwalejin ilimin kiwon kifi da ke New Bussa a jihar.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin NSCDC, ASC Nasir Abdullahi, ya fitar, The Nation ta ruwaito.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Sanarwar ta shaida wa manema labari cewa, an kama matashin ne a ranar 10 ga wannan watan ta Agusta bayan bin diddiginsa.
Ya hada baki da wani wajen yunkurin sace provost
Hakazalika, sanarwar ta kara bayyana cewa, matashin ba shi kadai ya yi aikin ba, ya hada baki ne da wani abokinsa da har yanzu ba kai ga kamowa ba.
An ce sun rubuta wasika ne, tare da turawa shugaban, inda suka nemi a basu kudi ko kuma su sace shi.
A bangare guda, sanarwar ba ta bayyana adadin kudin da matasan suka nema ba, amma dai dayan yana nan ana ci gaba da bincike.
Wani rahoton jaridar The Guardian ya bayyana cewa, yanzu haka an gurfanar da matashin a gaban kuliya domin hukunta shi kan laifukansa.
Jami'an sun ce matashin zai amsa laifuka biyu; hadin baki da kuma razana shugaban kwalejin da suka yi.
Ana kuma ci gaba da bincike don kamo dayan.
'Yan Sanda Sun Kama Wani Mutum Yana Zagin Kabarin Wata a Wani Faifan Bidiyo
A wani labarin, rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta cafke wani mutum mai suna Abdullahi Yar Dubu biyo bayan wani faifan bidiyon TikTok da ya nuna yana zagi da ruwan ashariya a kan kabarin mahaifiyar abokinsa.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa a ranar Lahadi ya tabbatar da cewa an kama ‘Yar Dubu tare da mika shi zuwa hedikwatar ‘yan sanda da ke Kano domin ci gaba da yi masa tambayoyi.
An ga ‘Yar Dubu a cikin faifan bidiyon yana tsaye a saman kabarin yana zagin mamaciyar da aka binne a wani lokaci a baya, rahoton Sahelian Times.
Asali: Legit.ng