Ruwa Yayi Awon Gaba da Dalibai 4 Dake Bidirin Kammala WASCCE a Gabar Teku

Ruwa Yayi Awon Gaba da Dalibai 4 Dake Bidirin Kammala WASCCE a Gabar Teku

  • Ruwa yayi awon gaba da dalibai hudu daga cikin 10 da suka je shagali da bidirin kammala jarabawar WASSCE a gabar teku
  • Mummunan lamarin ya faru ne a gabar teku ta Elegushi dake yankin Lekki a jihar Legas inda daliban suka faki ido suka shige
  • An gano cewa, daliban masu shekaru 14 zuwa 15 duk 'yan kwalejin Kuramo ne dake Lekki kuma an ceto 6 daga cikin 10 kadai

Legas - Mummunan lamari ya faru a gabar teku ta Elegushi dake yankin Lekki a jihar Legas bayan ruwa yayi gaba da matasa hudu dake iyo a wurin.

Punch ta rahoto cewa, dalibai 10 dake kammala sakandare masu shekaru 14 zuwa 15 ne suka je gabar tekun shagalin kammala rubuta jarabawar WASSCE dinsu.

Dalibai
Ruwa Yayi Awon Gaba da Dalibai 4 Dake Bidirin Kammala WASCCE a Gabar Teku. Hoto daga Punchng.com
Asali: UGC

Premium Times ta ruwaito cewa, an gano cewa, daliban kwalejin Kuramo ce dake Lekki.

Kara karanta wannan

Kano: Yara 3 Sun Mutu Yayin Da Dakin Mahaifiyarsu Ya Rushe Ya Rufta Musu

Mai magana da yawun hukumar gabar teku Elegushi, Cif Ayuba Elegushi, a wata takardar da ya fitar a ranar Talata, yace daliban basu da rijista a wurin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya sanar da cewa,lamarin ya faru ne a wani sashi na gabar tekun ba a cikin jama'a ba.

Ya ce:

"Da farko mun koresu daga wani yankin tekun da suka ce suna son yin iyo. Daga nan sai suka wuce wani wurin da babu jama'a. 'Dan wani 'dan uwanmu ne, Abbas, wanda ya dauko su daga makaranta kuma yaran suka biyo shi.
"Ba su biya kudin shiga wurin ba. Abbas yayi amfani da cewa yana daya daga cikinsu ya shigar da su ta wata hanyar."

An gano cewa, wadanda lamarin ya faru da su ne suka dinga ihu saboda ruwa ya fara tafiya da su.

Elegushi yace, wasu masu taimako ne suka fada ruwan tare da fito da sauran shidan a raye.

Kara karanta wannan

Abuja: An kame wasu mutane 480 da ake zargin sun tsere daga magarkamar Kuje

"Daga cikin shidan da aka ceto, wasu daga cikinsu sun tsere da muka je wurin. Mun samu kama biyu daga ciki kuma mun kai su ofishin 'yan sanda na Jakande.
"A yanzu haka, hudu daga cikin yaran sun bace saboda an kasa gano su a cikin ruwan. Mun sanar da iyayensu kuma sun iso ofishin 'yan sandan.
"Abbas yana daga cikin yaran da ba a gani ba. Akwai wani yaro daya da wasu yara mata biyu," ya kara da cewa.

Kakakin ya bayyana cewa, yaran biyu sun sanar da 'yan sanda cewa an fatattake su daga gabar tekun kafin su samu su saci hanya tare da shiga ta wannan bangaren da babu mutane.

Yace:

"A bayanin da suka rubuta a ofishin 'yan sandan, sun ce an fatattakesu a sashin farko. Abbas ne yace kada su damu zai kai su wani sashi. A nan ne ya kai su inda jama'a ba su nan."

Kara karanta wannan

Ku Daina Kashe Namun Dajin Dake Rayuwa A Fadar Aso Villa, Fadar Shugaban kasa ta koka

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Legas, Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da aukuwar lamarin inda yace suna cigaba da bincike..

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel