Namijin Kirki Ba Zai Yi Soyayya Da Budurwa Fiye Da Shekara Ba Tare Da Ya Aure Ta Ba – Hadimin Gwamna
- Hadimin gwamnan jihar Cross River, Andrea Ekeng Inyang, ya shawarci yan mata da su daina korar masu sonsu da niyar kirki
- Inyang ya ce babu namijin kirki da zai shafe shekara daya yana soyayya da mace ba tare da ya aure ta ba
- Matashin ya kuma shawarci mata da su daina anko da samari suna daukar hotuna da yada su a soshiyal midiya
Najeriya - Andrea Ekeng Inyang, hadimin gwamnan jihar Cross River, Ben Ayade, na musamman kan dabarun sadarwa, ya ja hankalin yan matan zamani a kan samarin kirki.
Inyang a wata wallafa da ya yi a shafinsa na Facebook, ya bayyana cewa namijin kirki ba zai taba soyayya da budurwa na fiye da shekara daya ba kafin ya aure ta.
Ya kuma shawarci yan mata da su daina anko da samarinsu suna yawo a titi kamar wasu mata da miji alhalin ba a daura masu aure ba.
A cewarsa, duk mace da yin anko da saurayi tare da watsa hotunansu a shafukan soshiyal midiya toh tana koran ainahin mazajen kirki ne da ke son da aure.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya rubuta a shafin nasa:
“Har sai an daura maki aure, ke budurwa ce a hukumance. Ku daina sanya anko kamar ma’aurata kuna yawo a unguwanni da watsa hotunanku a shafukan soshiyal midiya saboda kina koran ainahin wadanda za su aure ki. Mutumin kirki ba zai yi soyayya da ken a fiye da shekara day aba. Idan kin ga dama ki saurare ni, idan kin ga dama ki ci gaba da fadama mutane cewa kina cikin soyayya mai karfi.”
Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin jama'a a kasa:
Itiung Philip ta ce:
"Ekeng! shekaru nawa kayi soyayya da matarka kafin ka aure ta?."
Patrick Etim ya ce:
"Mun ji ka yallabai, amma duk da haka za mu yi abun da ke zuciyarmu idan soyayyar tayi mana dadi."
Mimmy Rejoice ta rubuta:
"Hmmm."
Faith Emmah ta yi martani:
"Ba kai za ka fada mana abun da za mu sa ba ."
Allah Ya Yi Mun Gamon Katar: Matar Aure Ta Wallafa Hotunan Mijinta Yana Tayata Girki A Icce
A wani labarin, wata matashiyar mata mai suna Misis Zanga a Twitter ta wallafa wasu hotuna don yabawa mijinta.
Matar a cikin wallafar da ta yi a ranar Lahadi, 14 ga watan Agusta, ta bayyana cewa mijinta yana taimakonta sosai da sosai.
Ta yi godiya ga Allah da ya bata mutumin a matsayin abokin rayuwa. A cikin hotunan, an gano mutumin ba riga yana taimakawa matar a cikin dakin girki.
Asali: Legit.ng