‘Yan bindiga da ‘yan kungiyar IPOB na barazana ga zaben 2023 – Dambazau

‘Yan bindiga da ‘yan kungiyar IPOB na barazana ga zaben 2023 – Dambazau

  • Yayin da ake ci gaba da fuskantar zaben 2023, tsohon babban hafson sojin Najeriya ya bayyana matsalolin tsaro
  • Dambazau ya bayyana barazanar da Najeriya za ta iya fuskanta a lokutan zaben 2023 da ke tafe
  • 'Yan Najeiya da dama na ci gaba da nuna damuwa da tambayar me zai iya faruwa a lokutan zabe

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Punch ta kawo cewa, tsohon babban hafsan soji kuma ministan harkokin cikin gida, Janar Abdulrahman Dambazau, ya bayyana cewa, matsalolin 'yan bindiga da na IPOB na iya zama babbar barazana ga zaben 2023 mai zuwa.

Danbazau ya fadi haka ne a lokacin da yake gabatar da wata takarda mai taken, “2023 Politics: National Security and Nigeria’s Stability” mai tsokaci game da tsaron Najeriya da zaman lafiya.

Ya gabatr da takardar ne a taron lacca na shekara-shekara na Jaridar Blueprint a Abuja ranar Talata 16 ga watan Agusta.

Kara karanta wannan

Karon Farko a Tarihi, Buhari Ya Kirkiro Sabon Mukami Domin Magance Rashin Tsaro

Rashin na iya zama matsala ga zaben 2023 mai zuwa
‘Yan bindiga da ‘yan kungiyar IPOB na barazana ga zaben 2023 – Dambazau | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

An tambayi Dambazau ko rashin tsaro da ake fuskanta zai shafi zaben 2023 mai zuwa? Daga nan ya amsa da cewa tabbas hakan zai iya shafar zaben.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kuma bayyana cewa, akwai al'umomin da za su iya fuskantar tsaiko wajen halartar zaben na 2023 mai zuwa, The Nation ta ruwaito.

Ya kara da cewa:

“Jami’an INEC da ma’aikatan wucin gadi za su ji tsoro sosai duk da tabbacin da gwamnati ta ba su na kare su.
"Samun damar zuwa ga rumfunan zabe a cikin al'ummomin kan iyaka na iya haifar da wasu matsaloli. Wannan shi ne karin dalilin da ya sa dole a samar da isasshen tsaro.”

Gwamnatin Buhari Ta Rage Ta’addanci Zuwa ‘Kusan Babu Komai’, Inji Keyamo

Kakakin yakin neman zaben shugaban kasa na jam'iyyar APC, Festus Keyamo, ya ce gwamnatin tarayya karkashin jam'iyyar ta rage karfin Boko-Haram zuwa "kusan babu komai."

Kara karanta wannan

Shawari kyauta: Hanyoyi 15 da za ku bi domin kiyaye kanku daga fadawa matsala a Najeriya

Keyamo, wanda kuma shi ne karamin ministan kwadago da samar da ayyukan yi, ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Trust. Ya kuma kare ayyukan gwamnatin APC a cikin shekaru bakwai da ta yi tana mulki.

Shirin ya kuma samu halartar Daniel Bwala, mai magana da yawun tawagar yakin neman zaben shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Premium Times ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.