Mustapha Gajibo Ya Kera Motocin Bas Masu Amfani Da Lantarki, Hotunan Sun Kayatar Da Mutane

Mustapha Gajibo Ya Kera Motocin Bas Masu Amfani Da Lantarki, Hotunan Sun Kayatar Da Mutane

  • Wani matashin dan Najeriya, Mustapha Gajibo, ya saki jerin sabbin motocin bas masu amfani da lantarki daga kamfaninsa mai suna Pheonix Renewables
  • Gajibo ya yi fice sosai kan kokarinsa da kuma sha’awarsa ga motoci masu amfani da lantarki wanda tuni ya kera wasu adadi da ake amfani da su a garin Maiduguri
  • Sabbin bas masu cin mutane 12 da ya saki suna amfani da lantarki ne dari bisa dari kuma suna aiki da hasken sola; hotunan motocin ya matukar kayatar da yan Najeriya

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Maiduguri - Yan Najeriya a soshiyal midiya sun cika da murnar ganin sabbin motocin bas masu amfani da lantarki wanda Injiniya Mustapha Gajibo ya kera a Maiduguri.

Gajibo wanda ya kasance sanannen injiniyan makamashi ya wallafa kayatattun hotunan sabbin motocin bas din a shafinsa na Twitter wanda ya burge mutane da dama.

Kara karanta wannan

Yajin ma'aikatan wuta: Gwamnati da TCN na rokon kada a sa 'yan Najeriya a duhu

Mustapha da motar bas
Mustapha Gajibo Ya Kera Motocin Bas Masu Amfani Da Lantarki, Hotunan Sun Kayatar Da Mutane Hoto: @mustapha_gajibo.
Asali: Twitter

Kaso 65% na kayayyakin da aka yi amfani da su wajen kera motocin daga gida Najeriya aka same su

An tattaro cewa sabbin motocin bas din mai cin mutum 12 zai iya gudun kilomita 212 bayan chaji daya tare da shafe tsawon kilomita 110 duk awa daya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bas din na kuma aiki kan hasken sola. Da yake wallafa hotunan a shafinsa na Twitter, Gajibo ya ce kaso 65 cikin dari na kayayyakin da aka kera motocin da su an same su ne a gida Najeriya. Ya rubuta:

“Kaso 100 na lantarki, kujerar mutum 12, shafe kilomita 212 a chaji daya, gudun kilomita 110 duk awa, cike da na’urar sanyaya wuri, na’urar murya, an kera su ta hanyar amfani da 65% na kayayyaki da aka nema a gida, an tsara tare da kera su a Najeriya.”

Kara karanta wannan

Da Izinin Allah Zan Fito Lafiya: Eedris Abdulkareem Yace Matarsa Ce Za Ta Bashi Kodarta

Kalli wallafarsa a kasa:

Jama'a sun yi martani

@Oluwalonsegun

"Allah ya yi maka albarka."

@MubarakJidda ta ce:

"A Maiduguri ."

@KehindeTech ya rubuta:

"Nawa dan Allah."

@Olusayo_Fad

"Aikinka ya yi kyau . za mu iya sanin farashin?. Nagode."

@UsmanIshaqa2 ya ce:

"Aikinka ya yi kyau sosai."

@mr_lams_lamido ya ce:

"Sannu da kokari injiniya, kasar nan na bukatarka musamman a irin wannan mawuyacin lokaci."

Kamar Almara: Bidiyon Na'urar Daukar Hoto Ta Sama Mai Siffar 'Super Man' Ta Girgiza Intanet

A wani labarin, wani bidiyon YouTube ya nuno lokacin da aka saki wani na’ura mai siffan ‘superman’ a sama.

A cewar tashar Caters Video, Lauya Everton Marcelo, mai shekaru 40, daga Ribeirao Preto, Brazil ne saki na’urar bayan wasu abokansa sun kera ta.

Na’urar ta lula can sama kamar yadda dai ake gani a cikin fina-finan Turai kuma hakan ya matukar bawa mutane mamaki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng