'Yan Bindigan da Suka Sace Kwamishinan Nasarawa Sun Nemi Kudin Fansa N100m
- Rahotanni sun karade gari cewa, kwamishinan gwamnan jihar Nasarawa ya samu tsaiko, 'yan bindiga sun sace shi
- 'Yan bindigar dai sun bayyana bukatar N100m a matsayin kudin fansa, kasa da haka kuwa ba za su karba ba
- Ba wannan ne karon farko da 'yan bindiga ke sace makusanta gwamnoni ko masu rike da mulki a kasar nan
Jihar Nasarawa - Wadanda suka yi garkuwa da kwamishinan yada labarai na jihar Nasarawa Lawal Yakubu sun bukaci a biya su N100m a matsayin kudin fansa.
Jaridar The Nation ta rawaito cewa an sace Yakubu ne a gidansa da ke karamar hukumar Nasarawa Eggon da yammacin ranar Litinin 15 ga watan Agusta.
Wata majiya mai tushe wacce ta nemi a sakaya sunanta, ta tona cewa masu garkuwa da mutanen sun bayyana bukatarsu ne a ranar Talata
Ya ce tsagerun sun kira da misalin karfe 4:30 na yamma ta wayar daya daga cikin iyalan kwamishinan, sun sha alwashin ba za su karbi kasa da N100m kafin su sako shi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cewarsa:
“A gaskiya sun bugo waya da yammacin yau da misalin karfe 4:30 na yamma suka bukaci a ba su N100m kuma a lokacin da ‘yan uwan suka nemi ba da N3.5m sai suka kashe wayar cewa ba da gaske suke ba kuma suka dage cewa duk abin da ya yi kasa da N100m kawai a mance da shi. Sun kira lambar amma ba ta shiga.”
Ya zuwa yanzu dai ‘yan sanda tare da hadin gwiwar rundunoni da dama a hukumar ciki har da jami'an sashin yaki da masu garkuwa da mutane, jami’an soji, ’yan banga da mafarautan yankin sun fara kokarin mamaye dazukan yankin, inji SaharaReporters.
Yan bindiga sun kashe ango, sun sace wasu da dama harda iyalan tsohon kwamishina a Kaduna
A wani labarin, wasu tsagerun yan bindiga a safiyar ranar Asabar, 28 ga watan Mayu, sun farmaki garin Jere a karamar hukumar Kagarko da ke jihar Kaduna, inda suka kashe mutum daya tare da sace wasu da dama ciki harda mutum hudu yan gida daya.
An tattaro cewa yan bindigar sun kashe wani sabon ango sannan suka yi awon gaba da matarsa wacce ke dauke da juna biyu.
Yan bindigar sun kuma yi garkuwa da wasu mutum hudu a ahlin Abdulrahman Ibrahim Jere, tsohon kwamishinan yaki da talauci a jihar, jaridar Punch ta rahoto.
Asali: Legit.ng