Gwamnatin Buhari Ta Rage Ta’addanci Zuwa ‘Kusan Babu Komai’, Inji Keyamo

Gwamnatin Buhari Ta Rage Ta’addanci Zuwa ‘Kusan Babu Komai’, Inji Keyamo

  • Jigo a tafiyar takarar Tinubu a APC ya magantu, ya ce jam'iyyar ta tabbatar kawo karshen rashin tsaro
  • Shugaba Buhari ya yiwa Najeriya alkawarin kawo karshen rashin tsaro, tare da yakar cin hanci da rashawa
  • Ya zuwa yanzu dai, Najeriya na ci gaba da fuskantar hare-hare daga 'yan ta'adda daga bangarori daban-daban

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

FCT, Abuja - Kakakin yakin neman zaben shugaban kasa na jam'iyyar APC, Festus Keyamo, ya ce gwamnatin tarayya karkashin jam'iyyar ta rage karfin Boko-Haram zuwa "kusan babu komai."

Keyamo, wanda kuma shi ne karamin ministan kwadago da samar da ayyukan yi, ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Trust.

Ya kuma kare ayyukan gwamnatin APC a cikin shekaru bakwai da ta yi tana mulki.

Kara karanta wannan

Kaunar da Nake wa 'Yan Najeriya Bata Misaltuwa, Shugaba Buhari

Kayemo ya magantu kan irin kokarin da Buhari a shekaru 7
Gwamnatin Buhari Ta Rage Ta’addanci Zuwa ‘Kusan Babu Komai’, Inji Keyamo | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Shirin ya kuma samu halartar Daniel Bwala, mai magana da yawun tawagar yakin neman zaben shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Premium Times ta ruwaito.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Alkawarin Buhari

Da Shugaba Muhammadu Buhari ya zama shugaban kasa 2015, jam’iyyar APC ta yi alkawarin tabbatar da bunkasar tattalin arziki, yaki da rashin tsaro da cin hanci da rashawa domin sake dawo da kasar nan kan turba.

Duk da munanan hare-haren da 'yan ta'adda ke kaiwa al'ummomi a wasu sassan kasar, musamman a Arewacin kasar, Keyamo ya ce gwamnati ta rage aukuwar ta'addanci sosai idan aka kwatanta da yadda kasar take a karkashin gwamnatin PDP.

Ya yi zargin cewa ‘yan adawa ne suka dauki nauyin wannan labaran da ke nuna gazawar gwamnati don bata sunan jam’iyya mai mulki.

Hakazalika, ya ce ai dama gwamnatin APC ta gaji Boko Haram a hannun PDP, kuma ya zuwa yanzu dai abubuwa sun lafa nesa ba kusa ba, kamar yadda The Cable ta kawo.

Kara karanta wannan

Peter Obi: Abin Da Zan Yi Bayan Na Lashe Zaben Shugaban Kasar Najeriya A 2023

Jigon na jam’iyyar APC ya ce:

"Labarin cewa gwamnati ta gaza ya zama wata waka da kusan 'yan adawa suka dasa a makogwaron kowa ba tare da duban cikakken abin da muka yi ba."
“Mun gaji matsalar Boko Haram. A lokacin sun kwace kananan hukumomi sama da 14 a yankin Arewa maso Gabas tare da kafa tutocinsu.
“Mun gaji rikicin manoma da makiyaya da ke faruwa tun kafin zamanin Obasanjo. Ba a kawar da Boko Haram kwata-kwata ba amma ya ragu matuka saboda mun kulla alaka da kasashen makwabta.
"Mun rage ta'addanci zuwa kusan babu shi."

Yan Bindiga da Masu Kai Musu Bayanai Za Su Fuskanci Hukuncin Kisa, Inji Matawalle Na Zamfara

A wani labarin, gwamnatin jihar Zamfara ta rattaba hannu a kan hukuncin kisa ga duk wanda aka samu da laifin aikata fashi da makami, satar shanu, tsafi, ko kai wa 'yan bindiga bayanan sirri.

Gwamna Bello Matawalle ne ya bayyana hakan a wani sako da ya sanarwa al’ummar jihar a safiyar ranar Talata 16 ga watan Agusta, Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ba gaskiya bane: Gwamna dan rashawa da Buhari ya yiwa afuwa ya musanta batun yin takara a 2023

Matawalle ya ce: “A ranar 28 ga watan Yuni na wannan shekara, na sanya hannu kan kudirin dokar haramtawa da hukunta masu fashi da makami, satar shanu, tsafi, garkuwa da mutane da sauran laifukan da sukashafe su, 2022.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.