Ayyiriri: Kyawawan Hotunan Jami’an Yan Sandan Najeriya Yayin Da Suka Shiga Daga Ciki

Ayyiriri: Kyawawan Hotunan Jami’an Yan Sandan Najeriya Yayin Da Suka Shiga Daga Ciki

  • Kyawawan jami’an yan sandan Najeriya biyu sun cika burukan zukatansu ta hanyar kulla aure a tsakaninsu
  • Zukekiyar amaryar ta wallafa kyawawan hotunansu wanda ke kunshe da labarin yadda suka fara soyayya
  • Mabiya shafukan soshiyal midiya sun nuna sha’awarsu da ganin kyawawan hotunan ma’auratan yayin da suka taya su murna

Najeriya - Mabiya shafukan soshiyal midiya sun taya wasu jami’an yan sandan Najeriya biyu murna yayin da suka shiga daga ciki.

Labaran masoyan ya yadu ne a shafukan soshiyal midiya bayan amaryar ta je shafinta na TikTok don baje kolin hotunansu.

Ta wallafa hotunansu iri-iri dauke da bayanin kowani lokaci a tafiyar soyayyarsu, ciki harda wani bidiyonsu sanye da kayan yan sanda yayin da suka je hirar aurensu.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Da Yawa Sun Mutu Yayin Da Suka Yi Yunkurin Kai Mummunan Hari Garuruwa Biyu a Jihar Katsina

Jami'an yan sanda
Ayyiriri: Kyawawan Hotunan Jami’an Yan Sandan Najeriya Yayin Da Suka Shiga Daga Ciki Hoto: TikTok/@qweenavid
Asali: UGC

Hoton farko na @qweenavid yana dauke da bayanin cewa sun fara soyayya ne bayan sun hadu a hukumar yan sandan.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Hoto na gaba ya nuno su a sansanin horar da yan sanda sannan wani ya nuno su sanye da inifam dinsu yayin da suka kammala makarantar yan sanda.

A cikin hotunan kafin aure da na lokacin aurensu, an gano masoyan yan sandan suna yiwa junansu kallon so mai cike da shaukin juna.

Kalli hotunansu a kasa:

Jama'a sun taya ma'auratan murna

amardez1 ta ce:

"Ina taya ku murna, Allah ya albarkaci gidanku."

user5038315491289 ya ce:

"Babu bukatar asarar kudi a kan kaya...kawai ku yi amfani da inifam...Na taya ku murna."

user9578629837752 ya ce:

"Baaba, babu wanda zai yi wargi a inda suke, kyawawan ma'aurata."

Tunda Kunzo A Daura Kawai: Daga Zuwa Kai Gaisuwa, Iyaye Sun Nemi A Shafa Fatiha Kowa Ya Huta, Bidiyo

Kara karanta wannan

Basa Taba Koyon Darasi: An Hasko Jami’an Yan Sanda Suna Karban Na Goro Daga Fasinjoji, Bidiyon Ya Yadu

A wani labarin kuma, mabiya shafin Twitter sun tofa albarkacin bakunansu bayan samun labarin wani aure da aka kulla ba tare da shiri ba kuma cikin sauki a karshen makon jiya.

Kamar yadda wani matashi mai suna Mista Bukhari Suwaid da shafin @suwaidybaba a Twitter ya bayyana, ya ce sun raka wani abokinsa gidan iyayen budurwar da yake nema da nufin gaisuwa.

Sai dai da isarsu gidan, sai iyayen suka nemi su je su zo da goro inda suka shiga kaduwa matuka. Bayan nan sai suka yi kamar yadda aka umurce su inda suka siya goro suka kai tare da bayar da kudin sadaki gaba daya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel