‘Yan Majalisar Dattawa Sun yi Magana a kan Yunkurin Radawa Kaduna Sabon Suna
- Sanata Uba Sani yace labarin da ke zagaye gari na canzawa jihar Kaduna suna ba gaskiya ba ne
- ‘Dan takarar Gwamnan yace an kirkiro wannan labari ne domin bata masa suna saboda zaben 2023
- Sanatan ya tabbatar da cewa babu kudirin kirkirar wata sabuwar jiha a majalisar dattawan Najeriya
Kaduna - Sanata Uba Sani ya fito ya yi magana a game da labaran da ake yadawa na cewa za a canzawa jihar Kaduna suna, za ta koma jihar Zazzau.
Da yake bayani a shafin Twitter a ranar Litinin, 15 ga watan Agusta 2022, Uba Sani ya karyata wannan labari da yake yawo, yace karya ce aka kirkira.
“Hankali na ya kai ga wani labarin karya, mai illa da iya jawo rikici da aka kitsa, yana yawo a shafukan sada zumunta na zamani
Ana cewa shugaba Buhari ya sa hannu a kudirin kirkiro jihar Zazzau, wanda ni da Sulaiman Abdu Kwari muka kai gaban majalisa.”
- Uba Sani
A jawabin da ya fitar, ‘Dan takaran gwamnan na jihar Kaduna yace ya yi mamaki da wasu mutane suka kirkiro wannan karya saboda tsabar adawar siyasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sani ya zargi wadannan mutane da neman tada zaune tsaye, ba domin komai ba sai nufin kawowa takararsa cikas bayan sun fahimci yana samun karbuwa.
Dole hukuma tayi bincike a kai
Leadership ta samu wannan jawabi, ta rahoto ‘dan majalisar yana cewa wajibi ne jami’an tsaro su yi bincike domin su bankado masu wannan danyen aiki.
Sanatan na Kaduna ta tsakiya yake cewa zai yi kyau a hukunya duk wanda aka samu da hannu wajen kawo wannan labarin da zai iya kai ga fitina a jihar.
“Ana hutu yanzu a Majalisar dattawa. Babu wannan kudiri a gaban majalisa. Ana kirkirar jiha ne ta kwamitin da ke yi wa tsarin mulki garambawul.”
“Saboda haka wannan labari danyen aikin masu neman jawo rigima ne, dole jami’an tsaro su yi bincike, dole ayi masu hukunci, domin darasi ga na baya.”
- Uba Sani
Matsayar Sulaiman Abdu Kwari
Legit.ng Hausa ta samu labari cewa mutanen Sanatan Arewacin jihar Kaduna, Sulaiman Abdu Kwari sun yi watsi da labarin, suka ce ba gaskiya ba ne.
Tun 2015, Abdu Kwari ne yake wakiltar shiyyar Zazzau a majalisar dattawa na kasa.
El-Rufai ya tsokano Obidients
Kun samu rahoto cewa maganar da Malam El-Rufai ya yi a kan Sojojin OBIdients a shafinsa na Twitter a ranar Litinin , ta fusata wasu daga cikinsu ainun.
Abin ya yi zafi har sai da wani Masoyin Peter Obi a kasar waje ya nemi Twitter ta goge maganar da Gwamnan ya yi, amma ba kamfanin bai amince ba.
·
Asali: Legit.ng