Basa Taba Koyon Darasi: An Hasko Jami’an Yan Sanda Suna Karban Na Goro Daga Fasinjoji, Bidiyon Ya Yadu
- Wani bidiyo ya yadu a shafukan soshiyal midiya inda aka gano wasu yan sanda suna karban na goro a hannun fasinjoji
- Kamar yadda ya bayyana a bidiyon sun sanya daya daga cikin fasinjojin ya tura masu kudin ta asusun banki bayan ya yi amfani da wayarsa
- Mutane da suka kalli bidiyon sun tofa albarkacin bakunansu inda suka ce yan sandan basa taba koyon darasi
Najeriya - Wani bidiyo da ke nuna jami’an yan sanda suna karban na goro daga wajen wasu fasinjojin mota ya yadu a shafukan soshiyal midiya.
A cikin bidiyon wanda ya yadu, an gano wasu jami’an yan sandan a zaune a cikin motar da suka tsayar yayin da wani ya tsaya a waje, shafin LIB ya rahoto.
Sai aka jiyo na wajen yana tambayan ko fasinjojin da ke cikin motar sun aika kudin.
“Ka tura? Ya shiga?” an dauki bidiyonsa a daidai lokacin da yake tambayan daya daga cikin fasinjojin wanda ya tabbatar da cewar ya aika.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kalli bidiyon a kasa:
Jama’a sun yi martani
Tuni jama’a suka shiga sashin sharhi domin yin martani kan wannan al’amari inda wasu da dama suka ce jami’an yan sandan basa taba koyon darasi.
Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin a kasa:
comedianprivilegedson ya yi martani:
“Wai shin wadannan yan sandan basu da wayoyi masu shiga intanet ne don ganin abubuwan da ke faruwa da takwarorinsu ne ko kuma dai kawai basa ganin mutuncin IGP ne.”
jennykishy ta ce:
“Basa koyon darasi…kora na kan hanya…”
danoliza ya ce:
“Basa jin magana .”
sheila__ck ta ce:
“Za a sake korar wani jami’in dan sanda. Yan sanda da cin hanci 5 da 6 ne.”
henr8409 ya ce:
“Yaushe za ku yi hankali?"
Saboda Tsaro: Ku Guji Gidajen Karuwai Da Mashaya, IGP Ya Gargadi Jami’an Yan Sanda
A wani labarin, babban sufeto janar na yan sanda, Usman Baba Alkali, ya shawarci Jami’an yan sandan kasar da su guji zuwa gidajen karuwai da mashaya don guje ma hare-haren miyagu.
Alkali ya bayar da shawarar ne yayin da yake jawabi ya Jami’an rundunar a Gombe yayin rangadin da ya yi a jihar.
A cewarsa, Jami’an yan sanda na cikin hatsari a yanzu, saboda suna samun barazana daga mayakan IPOB, Boko Haram, ISWAP, yan fashi da makami, masu garkuwa da matane da sauransu, jaridar Leadership ta rahoto.
Asali: Legit.ng