Yan Bindiga Sun Sace Kwamishinan Labarai Na Jihar Arewacin Najeriya

Yan Bindiga Sun Sace Kwamishinan Labarai Na Jihar Arewacin Najeriya

  • Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kutsa gidan Honarabul Yakubu Lawal Addah, kwamishinan labarai, al'adu da yawon bude ido na Jihar Nasarawa, sun sace shi
  • Majiyoyi daga iyalan kwamishinan sun tabbatar da afkuwar lamarin suna mai cewa a daren ranar Litinin misalin karfe 9 zuwa 10 maharan masu bindigu suka sace
  • Mai magana da yawun yan sandan Jihar Nasarawa, DSP Ramhan Nansel ya tabbatar da sace Honarabul Yakubu Lawan ya kuma ce an baza tawagar jami'an tsaro don su ceto shi

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Nasarawa - Yan bindiga sun sace kwamishinan labarai, al'adu da yawon bude ido, na Jihar Nasarawa, Mallam Yakubu Lawal.

Hoton Yan Bindiga
Yan Bindiga Sun Sace Kwamishinan Labarai Na Wata Jihar Arewacin Najeriya. Hoto: @LeadershipNGA.
Asali: Twitter

Jaridar Leadership ta rahoto cewa yan bindigan sun sace Lawal ne a gidansa da ke Nasarawa Eggon a daren ranar Litinin bayan sun yi harbe-harben bindiga.

Kara karanta wannan

Ministan Buhari: APC ta gyara kasar nan, kamar ba a taba ta'addanci ba

Majiya daga iyalan kwamishinan ya magantu

Wata majiya daga iyalan kwamishinan, wanda ba ta son a ambaci sunanta, ta tabbatar da afkuwar lamarin

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Majiyar ta ce yan bindigan da suka yi awon gaba da kwamishinan suna dauke da muggan makamai masu yawa.

Martanin yan sanda

Mai magana da yawun yan sandan Jihar Nasarawa, DSP Ramhan Nansel ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar, LindaIkeji ta rahoto.

A cewarsa, an sanar da jami'an rundunar da ke sintiri kan karar harbe-harben bindiga da karamar hukumar Eggon na Jihar Nasarawa a jihar.

Nansel ya ce jami'an yan sanda na Nasarawa Eggon sun garzaya zuwa wurin da abin ya faru, yayin da kwamishinan ya sanda, CP Adesina Soyemi nan take ya tura karin yan sanda na Mobile Force da Masu Yaki da Garkuwa da Sojoji da Yan Banga da Mafarauta.

Kara karanta wannan

Bidiyon Karamin Yaro Yayi Shiga Sak Tinubu, Yana Jawabi Zagaye da Hadimai

"Bayan isarsu wurin, an gano cewar yan bindigan da a ba san ko su wanene ba yayin da suke harbe-harbe sun shiga gidan Honarabul Yakubu Lawal Addah, sun yi awpn gaba da shi zuwa wurin da ba a sani ba."

Kakakin yan sandan ya ce tawagar jami'an tsaro sun bazama aikin bincike a yankin karkashin jagorancin Area Kwamanda na Akwanga, ACP Halliru Aliyu don ceto wanda aka sace tare da kama wadanda suka aikata laifin.

"Kwamishinan yan sandan ya kuma ce duk wani da ke da bayani mai amfani da zai taimaka a ceto wanda aka sace ya tuntube su a lambobi kamar haka: 08035951018, 08033806409, 08037461715 and 08036157659", sanarwar ta kara da cewa.

'Yan Bindiga Sun Sace Basarake Mai Sanda Mai Daraja Ta Ɗaya, Sun Nemi Maƙuden Kuɗi Na Fansa

A wani labarin, kun ji cewa an yi garkuwa da basarake mai sanda mai daraja ta daya a jihar Kogi, Adogu na Eganyi a karamar hukumar Ajaokuta, Alhaji Mohammed Adembe kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Ma'aikatan wutar lantarki za su sa 'yan Najeriya a duhu a wani sabon yajin aiki

Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka sace basaraken ne a ranar Talata a kan hanyar Okene zuwa Adogo, rahoton Vanguard.

Asali: Legit.ng

Online view pixel