Bidiyon Karamin Yaro Yayi Shiga Sak Tinubu, Yana Jawabi Zagaye da Hadimai

Bidiyon Karamin Yaro Yayi Shiga Sak Tinubu, Yana Jawabi Zagaye da Hadimai

  • Wani yaro karami 'dan Najeriya daga karamar hukumar Mayo Belwa ta jihar Adamawa ya yadu bayan yin shiga sak irin ta Tinubu
  • A gajeren bidiyon dake nuna yaron sanye da hular Yarabawa lankwasassa irin ta 'dan takarar APC, ya fito sak kamar tsara shi aka yi
  • Ma'abota amfani da soshiyal midiya sun bayyana cewa, yaron ya birgesu yayin da magoya bayan Tinubu suka ce bidiyon na nuna tsabar sunan da Tinubu yayi a arewa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Mayo Belwa, Adamawa - Wani karamin yaro daga karamar hukumar Mayo Belwa ta jihar Adamawa ya birge ma'abota amfani da soshiyal midiya bayan yayi shiga sak ta Tinubu.

Yaron da har yanzu ba a gano sunansa ba, ya yadu a gajeren bidiyon inda yake sanye da lankwasassar hular Yarabawa wacce Tinubu ya saba sanyawa.

Kara karanta wannan

Kaunar da Nake wa 'Yan Najeriya Bata Misaltuwa, Shugaba Buhari

Yaro Kamar Tinubu
Bidiyon Karamin Yaro Yayi Shiga Sak Tinubu, Yana Jawabi Zagaye da Hadimai. Hoto daga @officialBAT
Asali: UGC

Tinubu zai zama shugaban kasa, Masoyansa suka ce

An gan shi a bidiyon sanye irin gilashin da jigon APC din yake sanyawa na tsawon shekaru.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ba wai shi kadai ba, yaron ya cigaba da yawo a cikin tawaga da magoya baya kamar yadda aka kuma ganinsa yana jawabi ga taron jama'a a abinda yayi kama da wurin kamfen.

jama'a masu tarin yawa sun kalla bidiyon a Facebook yayin da wasu magoya bayan Tinubu suke ta murna kan ganin irin wannan abu ya faru da 'dan takararsu.

Jama'a sun yi martani

Oluwaseun Adeniyi yace:

"Jagaban shine zai zama Shugaban kasa na nan gaba, da sunan Yesu Almasihu..."

Ismail Adepeju yace:

"Godiya muke da kayi wannan abu, Asiwaju Bola Tinubu shine shugaban kasan mu a gaba da izinin Ubangiji."

Kara karanta wannan

Ke duniya: Matashin da ya durawa kabarin mahaifiyar abokinsa ashariya ya shiga hannu

Orudunsu Sunday yace:

"Karamin Tinubu, zaka zama babban mutum da sunan Yesu Almasihu. 'Yan arewa sune kwararru a harkar."

Badejo Adebowale Solomon yace:

"Zan so Tinubu yayi kamar yadda yayi yana gwamna. Ya zama shugaban kasa ga matasa idan ya zama shugaban kasa."

Charles Leedee yace:

"Ko ana so, ko ba a so, Bola Tinubu zai zama shugabannin kasan Najeriya nan da 2023 da izinin Ubangiji."

Ubangiji Yana Amfani da Buhari ne Wurin Ladabtar da 'Yan Najeriya, Yemi Forounbi

A wani labari na daban, Yemi Farounbi, tsohon ambasadan Najeriya a kasar Philippine, yace Shugaban kasa Muhammadu Buhari ladabtarwar ce daga Ubangiji da ake yi wa 'yan Najeriya.

The Cable ta ruwaito cewa, Farounbi ya sanar da hakan ne a ranar Asabar yayin da aka tattauna da shi a shirin gidan rediyo a Ayekooto a Splash 105.5FM.

Yace an ja kunnen 'yan Najeriya kan tarihin Buhari da kuma yadda ya garkame 'yan siyasa masu tarin yawa.

Kara karanta wannan

Goyon Kaka: Bidiyon Yar Karamar Yarinya Tana Kwaikwayon Kakanta, Harda Nade Hannu A Baya

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel