Mutum 2 Sun Mutu, 5 Sun Jikkata a Wani Hatsarin Mota a Jihar Anambra
- An samu aukuwar mummunan hadari a jihar Anambra, inda aka rasa rayukan mutum biyu tare da mutum biyar da suka raunata
- Hukumar kiyaye haddura sun tabbatar da faruwar lamarin, sun kuma bayyana yadda lamarin ya auku
- Ana yawan samun hadurran mota a Najeriya sakamakon gudun wuce kima daga direbobi ko kuma lalacewar hanya
Onitsha, jihar Anambra - Wani mummunan hatsarin mota ya yi sanadiyyar mutuwar mutane biyu yayin da mutane biyar suka samu raunuka munana daban-daban, Daily Trust ta ruwaito.
Hadarin wanda ya auku a ranar Lahadi da misalin karfe 8:45 na dare a kan hanyar Onitsha zuwa Awka a jihar Anambra, ya gama ne da wata babbar mota da kuma mota bas ta safara.
Wani shaidan gani da ido ya bayyana cewa direban bas din ya rasa yadda zai iya tuka motar ne, inda doki bayan babbar motar da ke gabansa a tsaye.
A cewarsa:
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
“Direban babbar motar ya yi ajiye motar ne bayan ta samu matsala kuma ya sanya allon alamar taka tsantsan a gaba da bayanta. Amma direban bas din da ke gudu ya kutsa kan motar daga baya a hadarin.”
Babban kwamandan hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC), Kwamanda Adeoye Irelewuyi, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya danganta lamarin da toshe hanyar mota da wuce gona da iri.
Ya ce an kai mamatan zuwa dakin ajiyar gawa, sannan wadanda suka jikkata zuwa asibiti domin kula da lafiyarsu.
Yayin da yake jajantawa iyalan mamatan tare da yi wa wadanda suka jikkata fatan samun sauki cikin gaggawa, Irelewuyi ya gargadin cewa, ya kama masu ababen hawa su daina gudun wuce kima tare da tabbatar da sun kiyaye dokokin hanya.
Ya ce:
“Wani direban wata babbar mota kirar Mack mai rajista: FKJ22XJ da wata mota bas Toyota Hiace mai lamba: GDD68ZP sun yi hatsari mota a ranar 14 ga Agusta 2022 da misalin karfe 20:45 na dare."
Hakazalika, ya ce hadarin ya rutsa da mutane 12 ne, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Innalillahi: Hadarin mota ya lakume mutane 11 a hanyar Zaria zuwa Kaduna
A wani labarin, mutane 11 ne suka mutu a wani hatsarin mota da ya auku a hanyar Zaria zuwa Kaduna da yammacin ranar Asabar.
An tattaro cewa hatsarin ya afku ne a lokacin da wata mota kirar Toyota Carina mai lamba KTL 251QG, ta kwace a kusa da Nuhu Bamalli Polytechnic da ke Zaria, Daily Trust ta ruwaito.
Kwamandan hukumar kiyaye hadurra na kasa da ke Zaria, Abubakar Tatah Murabus, wanda ya tabbatar da faruwar hatsarin ya ce an kwashe dukkan wadanda abin ya shafa zuwa dakin ajiyar gawa.
Asali: Legit.ng