Magu ya amsa tambayoyi a kan zargi fiye da 20 da ke kansa a fadar Aso Villa

Magu ya amsa tambayoyi a kan zargi fiye da 20 da ke kansa a fadar Aso Villa

A ranar Litinin, 6 ga watan Yuli, wani kwamiti da shugaban kasa ya kafa ya binciki mukaddashin shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu.

Ana jin kishin-kishin din cewa wannan kwamiti zai bada shawarar a sauke shugaban hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin Najeriya zagon-kasa daga kujerarsa.

Tsohon Alkalin kotun daukaka kara a Najeriya, Ayo Salami shi ne ya jagoranci wannan kwamiti da ya binciki Ibrahim Magu a fadar shugaban kasa.

Jaridar Daily Trust ta samu labari daga majiya mai karfi cewa an taso keyar Ibrahim Magu ne bayan korafin da ministan shari’a, Abubakar Malami ya yi a kansa kwanaki.

AGF Abubakar Malami SAN da hukumar DSS su na zargin Magu da karkatar da kudin da hukumar EFCC ta tattaro daga hannun barayi a Najeriya, da kuma facaka da dukiya.

Majiyar ta ce akwai zargi fiye da 20 a kan wuyan shugaban hukumar na EFCC wanda har yanzu ya ke matsayin shugaban rikon kwarya bayan majalisar tarayya ta ki tantance sa.

KU KARANTA: Babu gaskiya a zargin Mahadi Shehu - Gwamnatin Katsina

Magu ya amsa tambayoyi a kan zargi fiye da 20 da ke kansa a fadar Aso Villa
Ibrahim Magu
Asali: Facebook

A makon da ya gabata ne shugaban kasa ya kaddamar da wannan kwamiti a Abuja, kusan da Ibrahim Magu ne kwamitin na Ayo Salami ya yi karin kummalo.

Sauran wadanda ke cikin wannan kwamiti sun hada da tsohon DIG na ‘yan sanda, Mike Ogbizi. Kwamitin ya na da wakili daga ofishin NSA, DSS da sauran jami’an tsaro.

Kamar yadda mu ka samu labari, jami’an DSS sun yi gaba da Ibrahim Magu ne da rana tsaka bayan sun same shi a tsohon ofishin hukumar EFCC da ke Wuse 2 a babban birnin tarayya Abuja.

Jami’an tsaron sun nunawa Magu takardar goron gayyata domin ya hallara gaban kwamitin shugaban kasa, inda ya bukaci a ba shi dama ya bayyana a wani lokaci nan gaba.

Kamar yadda rahotanni su ka bayyana, jami’an ba su ba Magu wannan dama ba, su ka tursasa masa cewa dole sai ya amsa kiran da aka yi masa nan take.

Wani wanda ya ke kusa da shugaban na EFCC ya ce tun ba yau ba, an dade ana kokarin ganin Magu ya zo ya amsa zargin da ke kan wuyansa, amma ba ayi nasara ba sai ranar Litinin dinnan.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng