An Farmaki Fitaccen Marubuci, Salman Rushdie, Wanda Ya Yi Batanci Ga Annabi SAW

An Farmaki Fitaccen Marubuci, Salman Rushdie, Wanda Ya Yi Batanci Ga Annabi SAW

  • Wani mutumi ya farmaki Salman Rushdie, wanda ya yi ɓatanci ga Annabi Muhammad da wuƙa a kasar Amurka
  • Rahotanni sun ce mutumin ya yi bazata ya ruga da gudu zuwa kan dandamalin da Salman zai yi jawabi, ya rinka daɓa masa wuka
  • Fitaccen Marubucin ya shafe shekaru a ɓoye bayan ya rubuta wani Littafi da ya harzuƙa musulmai

Wani mutumi ya kai wa shahararren marubucin nan, Salman Rushdie, hari yayin da yake kan dandamali zai yi jawabi a ƙasar Amurka.

Marubucin, wanda aka shafe tsawon shekaru ana masa bazaranar kisa saboda ya rubuta wani littafi, 'The Satanic Verses,' da ake zargin ya yi batanci ga Annabi SAW, an farmake shi ne a wani gari dake yammacin New York.

Kara karanta wannan

Mutumin da aka daba wa wuka saboda batanci ga Annabi na can asibiti rai hannun rabbaba

Salman Rushdie.
An Farmaki Fitaccen Marubuci, Salman Rushdie, Wanda Ya Yi Batanci Ga Annabi SAW Hoto: BBCHausa
Asali: UGC

A wani bidiyo da Aljazeera ta wallafa, ta ce wani mutumi ya yi fitar burgu zuwa kan dandamalin da Marubucin ke shirin gudanar da Lakca, inda ya rinka bugunsa yana daɓa masa wuka.

Shaidun da lamarin ya auku a gaban su, sun ce mutumin ya farmaki Mista Rushdie ne yayin da ake gabatar da shi a gaban taron Jama'a.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bayanai sun nuna cewa mahalarta taron ne suka yi kokarin zuwa kan Dandamalin domin kai masa ɗauki, amma ana tsammanin an daɓa masa wuƙa a wuya.

A halin yanzu, ba'a san halin da Fitaccen marubucin ke ciki ba, amma 'yan sanda sun tabbatar da cewa an daɓa wa wani mutumi wuƙa, ba su fayyace ko waye ba a bayanan su.

Shaidu sun ce an ɗauke shi a Helikwafta domin zuwa a kula da lafiyarsa yayin da aka kama mutumin da ya kai masa farmakin.

Kara karanta wannan

'Yan Sanda Sun yi Ram da Shugaban Dalibai Bayan Yace Minista Bai yi Wanka ba Ya Gana da Shugaban Kasa

Waye Salman Rushdie?

Salman Rushdie, marubuci ne ɗan ƙasar Indiya, kuma ya fara shahara ne a shekarar 1981 bayan ya rubuta wani Littafi mai suna, Midnight's Children.

Sai dai bayan rubuta littafin The Satanic Verses a shekarar 1988, Marubucin ya shiga ɓuya na shawon shekaru saboda Littafin ya tunzura Musulmai, waɗan ke ganin batanci ne ga fiyayyen Halitta, Annabi Muhammad SAW.

Wasu rahotanni sun bayyana cewa mutane da yawa ne suka rasa rayuwarsu biyo bayan wani rikici da ya ɓarke kan kaddamar da Littafin, cikin waɗan da suka mutu har da wasu da suka fassara Littafin.

A wani labarin kuma Wasu Mutum Uku Sun Tsallake Rijiya da Baya a Hannun Mutane Bayan Asirin Su Ya Tonu a Abuja

Wasu yan Damfara guda uku sun tsallake rijiya da baya a hannun fusatattun mutane biyo bayan sa bakin yan sanda a Abuja.

Wata sanarwa da kakakin yan sandan FCT Abuja, Josephine Adeh, ta fitar, ta ce kwamishina ya yi Allah wadai da lamarin.

Kara karanta wannan

“Saboda Zafin Rana, Turawa Sun Gudu”: Dan Najeriya Ya Nuna Yadda Tituna Suka Zama Wayam A Turai

Asali: Legit.ng

Online view pixel