Yan Sanda Sun Ceci Wasu Yan Damfara Uku Daga Hannun Fusatattun Matasa a Abuja

Yan Sanda Sun Ceci Wasu Yan Damfara Uku Daga Hannun Fusatattun Matasa a Abuja

  • Wasu yan Damfara guda uku sun tsallake rijiya da baya a hannun fusatattun mutane biyo bayan sa bakin yan sanda a Abuja
  • Wata sanarwa da kakakin yan sandan FCT Abuja, Josephine Adeh, ta fitar, ta ce kwamishina ya yi Allah wadai da lamarin
  • A halin yanzun bayanai sun nuna cewa yan sanda na kan bincike kan abun da ya faru tun farko

Abuja - Hukumar yan sanda reshen babban birnin tarayya Abuja ta ceci wasu yan damfarar Intanet uku yayin da mutane suka so ɗaukar doka a hannun su a yankin Lokogoma.

Mai magana da yawun hukumar, Josephine Adeh, Ita ce ta bayyana haka a wata sanarwa da ta fitar ranar Alhamis, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yanzun Nan: Jirgin Sojojin NAF Ya Halaka Kasurgumin Ɗan Ta'adda, Alhaji Shanono, da Wasu 17 a Kaduna

Hukumar yan sanda.
Yan Sanda Sun Ceci Wasu Yan Damfara Uku Daga Hannun Fusatattun Matasa a Abuja Hoto: punchng.com
Asali: Twitter

Ta ce kwamishinan yan sanda mai kula da FCT Abuja, Mista Babaji Sunday, ya gargaɗi mutane su guji ɗaukar doka a hannu, inda ya ce ɗauƙar doka da nufin warware matsala jahilci ne.

Ya ce rahoton binciken da aka gudanar ya nuna cewa fusatattun mutanen sun hau kan waɗan da ake zargin ne bayan sun yi yunkurin damfarar wata mace.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kwamishinan ya ƙara da cewa waɗan da ake zargin sun tsallake rijiya da baya ne bayan jami'an yan sanda sun yi gaggawar shiga tsakani, kuma yanzu haka suna tsare a magarkamar yan sanda.

Mista Sunday ya yi Allah wadai da yunkurin mutane tare da kira ga mazauna da su rinka kai zuciya nesa suna kai ƙorafi domin barin gaskiya ta yi adalci kan kowane abu.

Ya kuma jaddada buƙatar da ke akwai a kowane lokaci a bar gaskiya ta yi halinta, ba tare da duba kowane irin ɗanyen aiki wani ya aikata ba.

Kara karanta wannan

Dubu Ta Cika: An Kama Masu Safarar Kwayoyi da Yan Bindiga Sama da 100 a Jihar Arewa

Ɗaukar doka a hannu babban laifi ne - CP

Kwamishinan hukumar yan sandan Abuja ya gargaɗi mutane da cewa ɗaukar doka a hannu babban laifi ne da doka ta tanadarwa hukunci.

Bugu da kari ya sanar da cewa a halin yanzun jami'ai na kan bincike don gano gaskiyar abun da ya faru, kamar yadda Guardian ta rahoto.

A wani labarin kuma Yan bindiga sun gamu da cikas yayin da suka yi yunkurin garkuwa da Basarake a Kano

Jami'an yan sanda da haɗin guiwar yan Banga sun fatattaki yan bindiga, sun kubutar da Basaraken da suka yi yunkurin sace wa a Kano.

Kakakin yan Sandan Kano, Abdullahi Kiyawa, ya ce sun ceci Dagacin Garin Babba, kuma sun kwato Babura uku.

Asali: Legit.ng

Online view pixel