An Kwamushe Wasu Mutane 480 da Ake Zargin Wasu Daga Cikin Sun Tsere Daga Gidan Yarin Kuje Sun Tsere

An Kwamushe Wasu Mutane 480 da Ake Zargin Wasu Daga Cikin Sun Tsere Daga Gidan Yarin Kuje Sun Tsere

  • Hukumomi a babban birnin tarayya a Abuja sun kame wasu mutane da ake zargi da aikata laifuka
  • Wasu tsageru sun kai farmaki gidan yarin Kuje, inda wasu fursunoni da dama suka samu hanyar tserewwa
  • Rashin tsaro a Najeriya na kara kamari a wannan lokaci, lamarin da ke jawo cece-kuce a tsakanin 'yan Najeriya

FCT, Abuja - Jaridar Punch ta ruwaito cewa, hukumar babban birnin tarayya Abuja ta kama wasu mutane 480 da ake zargi da barnace-barnace a wasu gine-gine da ba a kammala gina su ba a yankunan Maitama da Wuse II.

Tun bayan harin magarkamar Kuje jami'an tsaro a Najeriya, musamman babban birnin tarayya suka fara bincike mai tsanani a yankuna daban daban.

Wdanda aka kama a wannan karon an ce suna buya ne a gine-gine da gidajen da ba a kammala a wasu yankunan birnin a matsayin mafakar aikata laifuka.

Kara karanta wannan

Daga karshe: An kama wadanda ake zargin sun shiga ofishin gwamnan Katsina sun sace miliyoyi

An kama wasu da ake zargin 'yan ta'adda ne a Abuja
Harin magarkama: An kwamushe was mutane 480 da ake zargin Kuje sun tsere | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Kwamandan da ke kula da rundunar, Mista Bennett Igweh, ya ce an kama mutanen ne dauke kayayyakin aikata lafuka da suka hada da wayaoyin hannu, bindiga, adduna, layu da dai sauransu, rahoton jaridar Leadership.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wasu sun gudu daga magarkamar Kuje

A cewar Igweh, rundunar ta dasa alamar tambaya kan wadanda aka kame, inda ya ce tana zargin wasu daga cikinsu sun tsere ne daga gidan yarin Kuje

Hakazalika, ya ce rundunar za ta yi bincike don gano asalin wadannan mutane tare da sanar da al'umma sunayensu.

A ci gaba da yunkurin kare birnin, ya kara da cewa za a ci gaba kwamushe a kauyuka 21 daga Kabusa zuwa Gishiri zuwa Waru da Wasa da sauran su a babban birnin tarayya.

Harin Gidan Yarin Kuje: Na Gargadi Aregbesola Kan Harin, Dakta Sadiq

Dakta Sadiq Amali na sashin nazarin halayar mutane a Jami'ar Tarayya ta Jigawa ya bayyana cewa ya yi hasashen za a kai hari gidan yarin Kuje a Abuja, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Dubu Ta Cika: An Kama Masu Safarar Kwayoyi da Yan Bindiga Sama da 100 a Jihar Arewa

Yayin da ya ke magana kan harin a shirin Sunrise Daily na Channels TV, Dakta Amali ya ce ya rubuta wasika ga Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbsola, game da yiwuwar kai harin.

Yan bindiga da ake kyautata zaton yan ta'adda ne, daruruwansu sun kai hari gidan yarin a ranar Talata da dare.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.