Bankin Duniya Ya Lissafa Kasashen Afirka 34 da Ke da Tarin Bashi Kuma Ka Iya Samun Yafiya
- Bankin Duniya da Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF) sun saki jerin sunayen kasashen duniya da ke da dimbin basussuka akansu
- A cewarsu, kasashe 39 da ke cikin jerin, 34 na Afirka ne kuma sun cancanci a yafe wasu wadannan basussuka
- Hakazalika, jerin ya bayyana ka'idojoji da sharuddan da kasashen za su bi wajen saryar da wannan bashi mai yawa
A cewar wani rahoton Business Insider, akwai kasashe matsakata karfi 34 a Afirka da ke da dimbin basussuka akansu.
Jerin ya fito ne karkashin wani shiri na hadin gwiwa na Bankin Duniya da Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF).
An dai kaddamar da shirin ne a 1996. Bayanai daga asusun IMF na cewa, shirin na son tabbatar da cewa babu wata kasa matsakaiciya da za ta fuskanci nauyin bashin da ba za ta iya sarrafa kanta ba.
Kasashe 39 a duniya da suka shiga jerin sunayen IMF da Bankin Duniya
Yunkurin yafe basussukan yana aiki ne ta hanyar kungiyoyin kudi da yawa ciki har da masu ba da lamuni na duniya kuma suna hadin gwiwa da gwamnatocin kasashen ne don rage basussukan waje zuwa matakan da za a iya sarrafawa.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Daga cikin kasashe 39 da ke cikin jerin, 34 kasashe ne na Afirka kuma suna da adadin mutane kusan miliyan 760 a jumillance.
Kasancewarsu kasashen da aka ce suna fama da fatara ba shine ma'aunin shiga jerin kasashe masu fama da bashi mai yawa ba. Sauran sharuddan sun hada da ingantaccen tarihin iya yakar fatara.
Lissafin IMF ya nuna cewa dole ne kasashe su cancanci karbar lamuni daga Hukumar Raya Kasashe ta Bankin Duniya.
Ga dai jerin kasashen kamar haka
- Ghana
- Tanzaniya
- Habasha
- Benin
- Burkina Faso
- Burundi
- Kamaru
- Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya
- Chadi
- Tsibirin Comoros
- Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo
- Jamhuriyar Kongo
- Ivory Coast
- Eritrea
- Habasha
- Gambiya
- Gini
- Guinea-Bissau
- Laberiya
- Madagascar
- Malawi
- Mali
- Mauritania
- Mozambique
- Nijar
- Rwanda
- Sao Tome da Principe
- Senegal
- Saliyo
- Somaliya
- Sudan
- Togo
- Uganda
- Zambiya
Jerin Kasashen Afrika 7 da dan Najeriya zai iya zuwa a Mota
A wani labarin, akwai wasu kasashe dake iyaka da Najeriya da mutum zai iya zuwa a mota don yawon bude ido ba tare da hawa jirgi ba.
Tafiya a mota na da amfani matuka saboda mutum zai iya ganewa idonsa abubuwa daban-daban tare da iya daukan hotuna sabanin jirgin sama.
Domin fita daga Najeriya da mota, ana bukatar mutum ya mallaki Fasfot, katin zama dan kasa, da kuma katin shaidan kayi rigakafin zazzabin Yellow Fever, sai kuma isasshen kudi.
Asali: Legit.ng